Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane Amma Suka Gamu Da 'Bakin Ciki'

Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane Amma Suka Gamu Da 'Bakin Ciki'

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kutsa gidajen mutane a Funtua a daren ranar Juma'a sun sace wasu amma sun gaza shiga wani gida
  • Wani faifan bidiyo da aka nada da na'urar daukan bidiyo na sirri ta CCTV ta nuna yadda yan bindigan suka so shiga wani gida amma suka kasa
  • Wani abokin mai gidan da suka kasa shigan ya ce mai gidan da iyalansa suna Abuja amma ya hada na'urar ta CCTV da wayarsa don haka ya ga abin da ya faru

Katsina - Wani bidiyo na na'urara CCTV ya nuna yadda wasu gungun yan bindiga suka kutsa wani gida a Funtua, Jihar Katsina a daren ranar Juma'a.

Yan bindigan, wanda bisa alamu sun so sace wasu ne, sun taho kauyen misalin karfe 10 na dare kuma suka fara kutsa gidaje suna sace mutane.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan Bindiga Sace Mata Masu Juna 2, da Mutum 13 a Sabon Hari

Yan Bindiga
Bidiyo: Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane Amma Suka Gamu Da 'Bakin Ciki'. Hoto: @daiy_nigerian.
Asali: Twitter

Daily Nigerian ta tattaro cewa yan bindigan ba su yi nasarar cimma burinsu ba a wani gida inda suka tara masu gidan sun tafi Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Ahmed Abdulkadir, abokin mai gidan (an boye sunansa), bayan sun yi harbi a kofar, sun shiga cikin gidan amma ba su tarar da kowa ba.

Mista Abdulkadir, wani tsohon direkta na NBC, ya rubuta a shafinsa na Facebook:

"Sun balle kofar gidan misalin karfe 10.20 na dare kamar yadda agogon CCTV kyamara ya nuna.
"An gode Allah, abokina da iyalansa ba su gari kuma mai gadin da ya lura ba lafiya sai ya tsere gidajen makwabta.
"Abokina, wanda injiniya ne da lantarki kuma ya san harkar sadarwa ta zamani, ya saka na'urar CCTV a gidansa wanda ke nuna masa komai a wayansa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Matashi Dan Shekaru 15, Ya Ce Mawaki Davido Ba Zai Iya Siyan Irinsa Ba

Ya cigaba da cewa:

"Bayan balle gate din gidan, sun kasa shiga cikin ainihin gidan, duk da kokarin harbin kofar da suka yi kamar yadda aka gani a bidiyon.
"Cikin fushi, ba su da wani zabi dole suka tafi. An ce sun huce fushinsu a gidajen Project Quarters, Funtua, inda suka sace mutane da dama."

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen suna adabar Funtua, Bakori da kauyukan da ke makwabtaka da su.

Ya yi Addu'ar Allah ya kawo mana dauki ya magance mana wannan matsalar.

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta'adda Suka Fitar

A wani rahoton, fadar shugaban kasa ta yi martani kan bidiyon da yan ta'adda suka fitar na barazanar cewa za su tarwatsa Najeriya, tana cewa jami'an tsaro ba su 'gaza ba kuma basira bata kare musu ba', rahoton Daily Trust.

Yan ta'addan sun fitar da bidiyo inda suka yi barazanar cewa za su sace Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

Asali: Legit.ng

Online view pixel