A ƙarshe, Birtaniya Ta Tsoma Baki kan Tsare Tsaren Tattalin Arzikin Tinubu a Najeriya
- Gwamnatin Birtaniya ta yi magana kan tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu tana cewa suna kara janyo jari da bunkasa kasuwanci
- Jakadan Birtaniya ya ce sauye-sauyen sun hada da cire tallafin maida hada tsarin canji, yana mai cewa hakan yana inganta shigar da jari
- Yarjejeniyar ETIP da jari daga Birtaniya a bangarori kamar na makamashi na kara tabbatar da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Gwamnatin Birtaniya ta yaba wa Najeriya bisa irin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi.
Gwamnatin ta ce tsare-tsaren na da muhimmanci wajen bunkasa ci gaba mai dorewa da kuma kyautata yanayin kasuwanci ga hadin gwiwar kasa da kasa.

Asali: Facebook
Tattalin arziki: Birtaniya ta yabawa Tinubu
Da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja, Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery, ya jinjina wa jajircewar gwamnatin Najeriya, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce gwamantin ta yi kokari wajen aiwatar da sauye-sauye da ya ce sun yi daidai da kudurin bunkasar tattalin arzikin Birtaniya.
Ya ce:
“Mun yaba da kokarin sauye-sauyen da gwamnatin Najeriya ke yi, musamman a karkashin shirin tattalin arzikin Shugaba Tinubu mai bangarori 8.
“Mun san an cire tallafin mai, mun san an daidaita tsarin canjin kudin waje, kuma babbar matsayata yau ita ce sauye-sauyen nan na haifar da riba.
“Na fahimci cewa wasu daga cikin wadannan sauye-sauyen suna da wahala ga talakawa.
“Farashin kaya har yanzu yana da tsada, yana tsakanin kaso 20 zuwa 25. Zai dauki lokaci kafin a rage hauhawar farashi, amma muna da yakinin cewa nan da watanni ko shekaru, hauhawar farashin kayayyaki zai ragu."

Asali: Getty Images
Gudunmawar Birtaniya domin inganta Najeriya
Wadannan kalamai na Montgomery sun biyo bayan yarjejeniyar hadin gwiwar kasuwanci ta ETIP da aka kulla tsakanin Najeriya da Burtaniya a watan Fabrairun 2024.
Montgomery ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “tsarin hadin gwiwa na gaske” da zai taimaka wajen habaka tattalin arziki da saukaka dokokin kasuwanci.
A karkashin yarjejeniyar ETIP, kasashen biyu na aiki tare a bangarori guda takwas da suka hada da noma, lafiya, hada-hadar kudi da ayyukan shari’a.
Haka kuma yarjejeniyar na neman saukaka ayyukan kwastam da kuma kyautata dokokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, The Nation ta ruwaito.
Montgomery ya bayyana wasu sababbin zuba jari da gwamnatin Birtaniya ta yi a Najeriya, ciki har da $40.5m a bangarori da dama.
Wani muhimmin cigaba shi ne saka fam miliyan 1.9 na Sankore domin tallafawa bincike da kirkire-kirkire a Najeriya.
Tinubu zai dauki dubban matasa aiki
Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da kafa sababbin jami’an tsaron dazuka domin kare Najeriya.
Majiyoyi sun ce za a dauki dubban matasa aiki a wannan sabon tsarin da gwamnatin tarayya da jihohi ke kokarin aiwatarwa.
Ma’aikatar Muhalli da ofishin Nuhu Ribadu za su jagoranci daukar ma’aikatan da kuma aiwatar da tsarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng