Tinubu zai Dauki Dubban Matasa Aiki domin Tsaron Dazukan Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa sababbin jami’an tsaron dazuka domin kare jejin Najeriya daga ‘yan ta’adda da miyagu
- Za a dauki matasa masu yawa aiki a wannan sabon tsarin da gwamnatin tarayya da jihohi ke kokarin aiwatarwa a Najeriya
- Ma’aikatar Muhalli da Ofishin Mai ba da Shawara kan Tsaro (NSA) za su jagoranci daukar ma’aikatan da kuma aiwatar da tsarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kafa jami’an tsaron dazuka domin tinkarar kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya.
Wannan mataki ya biyo bayan karuwar hare-hare daga ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ke fakewa a dazuka suna kai farmaki a jihohi daban-daban.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda shirin zai gudana ne a cikin wani sako da ma'aikatar muhalli ta wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da ta fito ne daga ma’aikatar muhalli da kuma ofishin mai ba da shawara kan tsaro ta ce an kusa kammala shirye-shirye don daukar matasa aikin.
Bola Tinubu zai dauki dubban matasa aiki
Shugaban kasa ya umurci hukumomi da su tabbatar da cewa jami’an da za a dauka za su samu horo na musamman da kuma kayan aiki na zamani.
An bayyana cewa daruruwan dazuka 1,129 da ke fadin Najeriya ne za a raba jami’an domin kare su daga masu laifi da ke amfani da su a matsayin mafaka.
Shugaban kasa ya ce gwamnatinsa ba za ta bar ko yanki guda na kasar nan a hannun ‘yan ta’adda ba, kuma wannan runduna za ta taimaka wajen karbo dazuka daga hannun masu laifi.
Hadakar gwamnatin Tinubu da jihohi
Daukar ma’aikata da gudanar da aikin tsaron zai kasance hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin tabbatar da ingantaccen tsaro a ko’ina.
An umurci Ma’aikatar Muhalli da kuma Ofishin Mai ba da Shawara kan Tsaro da su jagoranci daukar ma’aikata da kuma tabbatar da cewa ana bin ka’idoji wajen aikin.
Wannan mataki zai ba matasa damammaki na aiki da kuma kara tallafa wa kokarin gwamnati na yaki da ‘yan ta’adda da miyagun laifuffuka.

Asali: Twitter
Tinubu ya sha alwashin kwato dazukan Najeriya
Shugaban kasa ya bayyana cewa ba za a bar ‘yan ta’adda su yi amfani da dazukan Najeriya wajen aikata laifi ba, kuma rundunar da za a kafa za ta tabbatar da haka.
Ya kara da cewa gwamnati za ta kwato dazukan kasar nan domin hana keta haddi da kashe-kashen da ke yawan faruwa musamman a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
A cewarsa, rundunar za ta kasance ginshiki wajen hana ‘yan ta’adda mafaka da kuma kare al’umma daga hare-haren da suka addabi sassan kasar nan.
Dangote zai dauki matasan Najeriya aiki
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin Dangote ya bude kofa ga matasan Najeriya domin samun gurbin aiki.
Kamfanin Dangote ya ce za a dauki matasan da suka kammala karatun digiri a jami'a ko HND a kwalejoji.
An bayyana cewa duk wanda ya samu shiga aikin zai samu gogewa da horo daga kwararrun ma'aikatan kamfanin Dangote.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng