Jigon APC Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Mayar da Su Saniyar Ware a Raba Mukamai

Jigon APC Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Mayar da Su Saniyar Ware a Raba Mukamai

  • Babba a jam'iyyar APC, Dr. Mohammed Santuraki ta bayyana rashin jin dadinsa a kan yadda gwamnatin tarayya ta yi nadi a NCDC
  • Ya bayyana cewa duk da jiharsa ta Neja ta kawo kuri’u sama da 375,000 ga Bola Tinubu a zaben 2023, an ware su a nadin da aka yi
  • Dr. Santuraki ya kara da koka wa da cewa sun fi karfin makamai biyu da aka ba jiharsa a hukumar raya yankin Arewa ta Tsakiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Wani babban jigo a APC daga jihar Neja, Dr. Mohammed Santuraki, ya zargi gwamnatin tarayya da nuna bangaranci da rashin adalci wajen nade-nade.

Ya yai zargin cewa an nuna wariya a wajen nadin shugabanni a sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya, NCDC.

Tinubu
An zargi shugaban kasa da ware yan APC na jihar Neja a sababbin mukamai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa Dr. Santuraki, wanda shi ne Sakataren Kungiyar Masu Ruwa da Tsaki na Kudu ta Jihar Neja, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane yadda aka yi nadin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa tsarin nadin ya fifita wasu jihohi a kan wasu ba tare da la’akari da daidaito da adalci ba.

An yi tir da nadin da Tinubu ya yi a NCDC

Jaridar Punch ta wallafa cewa Dr. Santuraki ya ce an bar jihar Neja a baya a rabon mukaman ya uk da irin dimbin goyon bayan da ta bai wa jam’iyyar APC a zaben 2023.

Ya ce an yi watsi da su wajen raba manyan mukaman hukumar guda biyu da suka hada da Shugaban Hukuma da Manajan Darakta.

Ya ce:

“Duk da cewa jihar Neja ta samu mukamai biyu – Darakta da ba mai gudanarwa da kuma wani Daraktan Gudanarwa, wannan bai kai matakin da ya dace ba duba da rawar da jihar ta taka."

'Jihar Neja ta taimaki Tinubu,' Santuraki

Dr. Santuraki ya bayyana cewa jihar Neja ta kawo kuri’u sama da 375,000 ga Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023, wanda shi ne mafi girma a duk fadin yankin Arewa ta Tsakiya.

Ya kara da cewa APC ta lashe kujerun Sanata biyu cikin uku a jihar, ta samu sama da 70% na kujerun majalisar wakilai, sannan ta yi nasarar fitar da gwamna karkashin jam’iyyar.

Ya kuma tunatar da cewa jihar Neja ce ta fara neman a kafa hedkwatar hukumar NCDC a cikinta, amma daga baya ta janye bukatar ne domin bai wa jihar Nasarawa dama.

Tinubu
Jigon APC ya ce Tinubu ya ki duba taimakon da jihar Neja ta ba shi Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Dr. Santuraki ya ce:

“Abin da muke sa ran samu ya bayyana: Cewa a sakawa jihar Neja da akalla daya daga cikin manyan mukaman hukumar biyu. Abin takaici, hakan bai samu ba.”

An gano dabarun Tinubu na nakasa adawa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kaddamar da wani sabon tsari na siyasa da nufin karya karfin abokan hamayyarsa, kamar su Atiku Abubakar da Peter Obi.

Rahotannin sun bayyana cewa shugaban yana kokarin kafa karfi a yankin Kudu maso Gabas – inda Peter Obi ya fi karfi, tare da yunkurin rage tasirin Atiku da Obi a jihohi biyar na kasar nan.

Yanzu haka, jihohi biyu daga cikin biyar da ke yankin Kudu maso Gabas na karkashin jam’iyyar APC, kuma Tinubu ya fara kafa kawance da gwamnoni uku na sauran jihohin don samun nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.