“Karuwai Ba Sa Sauyawa”: Martanin Jama’a Bayan Saurayi Ya Kama Budurwarsa Tana Karuwanci a Otal

“Karuwai Ba Sa Sauyawa”: Martanin Jama’a Bayan Saurayi Ya Kama Budurwarsa Tana Karuwanci a Otal

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya da tuni aka gama zancen aurenta tsakanin iyayenta da na saurayinta ta jawo abin kunya
  • Sauyin nata ya gwadata, inda yasa aka yi masa kawalcinta zuwa otal ba tare da ta san shi bane, kwatsam kuma ta zo
  • Mutane da yawa da suka ga bidiyon sun shiga mamakin yadda za ta ci gaba da neman maza saboda kudi ga kuma batun aurenta

Wani bidiyon da aka yada a TikTok ya nuna rikicin da ya faru da wani mutumin da ya gwada budurwarsa don gano da gaske tana taba karuwanci.

Mutumin ya hada baki da ‘yar TikTok, @soniaolauzoma, wacce ta yi basaja a matsayin mai aiki da manya, inda ta samo budurwar tare da cewa za ta hada ta da wani su kwana ya ba ta kudi.

Kara karanta wannan

Wata Uwa Ta Koka Bayan Karamin Danta Ya Zubar Da Madarar N16k a Kasa, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

A ranar da suka gama shiri, mutumin ya jira a dakin otal, inda ya yi kamar dama yana jiran a kawo masa abokiyar alfasha ne.

Saurayi ya kamata budurwarsa a otal tana karuwanci
Yadda budurwa ta shiga hannu dumu-dumu | Hoto: @soniaolauzoma
Asali: TikTok

Kwatsam budurwarsa ta shigo, lamarin da ya bata masa rai sosai, a ce matar da zai aura tana karuwanci. A cewarsa, a cikin watan Afrilu ne za a yi aurensu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A lokacin da ta shigo kana ta tabbatar asirinta ya tonu, sai ta durkusa tana neman gafara tana zabga kuka.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

A kasa mun tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa bayan ganin bidiyon:

Sabie:

"Ina ganin laifin mazan da ke ganin ba mace kudi zai sa ta yi masa biyayya, idan mace bata da tarbiyya da kuma godiyar Allah, idan Allah ya hada ka da irinta ta gudu.”

Kara karanta wannan

“Ka Duba Darajarmu Idan Ta Yi Laifi”: Bidiyon Uban Amarya Yana Yi Wa Surukinsa Nasiha Mai Tsuma Zuciya a Ranar Aurensu

Your boyfriend atm holder:

"Tun da kake nemanta baka yi kokari kama ta ba sai da kuka gama shirin aure, lallai baka da wayo.”

timidare602:

"Lokacin da ya gwada ta ba komai bane...maganar shi ne meye yasa take karuwanci a lokacin da ta san ta kusa aure...”

CNJ:

"Kullum ina yawan magana. Karuwai ba sa sauyawa.”

StephanieNC:

"Da gaske mutumin yana sonta. Ya ji zafi a zuciyarsa.”

Ba zan iya auren mai albashin N70k ba

A wani labarin, bidiyo ya nuna budurwar da ke cewa, ba za ta iya auren saurayin da ke samun N70k a wata ba.

A cewarta, kudin ya yi kadan ya rike gida balle kuma maganar kula da abubuwan da suke da alaka da aure.

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani, sun bayyana yanayin da suke ciki a lokacin da suka yi aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel