Gwamna Bago Ya Shiga Coci, Kalaman da Ya Furta a ciki Sun Tayar da Ƙura

Gwamna Bago Ya Shiga Coci, Kalaman da Ya Furta a ciki Sun Tayar da Ƙura

  • GwamnanNiger, Umar Bago, ya janyo cece-kuce bayan shiga cikin cocin 'Living Faith' a birnin Minna da ke jihar
  • Bago, wanda ake kira gwamnan noma, ya ba da tallafin N50m da alkawarin gyara hanyoyin cikin harabar cocin domin kyautata musu
  • Jama’a sun rarrabu kan furucinsa, wasu na goyon baya, wasu kuma na sukar irin yadda ya nuna goyon baya ga addinin Kirista

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Gwamnan Jihar Niger, Umar Bago, ya jawo martani daban-daban daga ‘yan Najeriya bayan shiga coci har ya yi wasu kalamai.

Gwamnan ya bayyana kansa a matsayin 'tubabbe' a cikin cocin 'Living Faith' da ke birnin Minna a jihar Niger da ke Arewacin Najeriya.

Gwamna Bago ya jawo ka-ce-na-ce bayan kalamansa a coci
Gwamna Umaru Bago ya bayyana kansa a matsayin sabon tuba a cikin coci. Hoto: @HonBago.
Asali: Facebook

Musabbabin zuwan Gwamna Bago coci a Niger

Gwamnan ya bayyana hakan ne a bidiyo lokacin da ya kai ziyara cocin 'Liberation Mandate' a Minna da Theo Abu ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bago, wanda ake kira gwamnan manoma, ya bayar da gudummawar N50m tare da alkawarin gina hanyoyi cikin harabar cocin.

An ce gwamnan wanda Musulmi ne, ya halarci bikin cikar cocin shekaru 44 inda ya bayyana wannan kalma yayin jawabi ga jama’ar cocin.

Gwamna Bago ya shiga coci a Minna
Gwamna Umaru Bago ya bayyana kansa a matsayin tubabbe wanda ya jawo maganganu a Najeriya. Hoto: @HonBago.
Asali: Twitter

Martanin mutane kan kalaman Bago a coci

Bayan hakan, mutane da dama sun fara bayyana ra’ayoyinsu daban-daban dangane da yadda gwamna Bago ya fito fili ya yi wannan magana.

Wasu daga ciki sun yaba masa da cewa ba shi da ra'ayi mai tsauri yayin da wasu ke kushe yadda aka raina coci a Najeriya.

Har ila yau, wasu daga cikin masu sharhi kuma na sukar gwamnan duba da yadda ya nuna goyon baya ga addinin Kirista a matsayinsa na Musulmi.

Cif CeeKee ya rubuta:

"Ba daidai ba ne coci ta bari a raina addinin Kirista haka. Gwamna ya tsaya kawai kan abin da ya kawo shi."

Beee ya yabawa gwamnan:

"Yin haka da fara’a na nuna halin dan adam a cikinsa. Wannan na kawo hadin kai da ci gaban Najeriya."

Obi Daniel Ebuka ya rubuta:

"Tun lokacin sakandare na san shi da suna Abu LOLO. Shi ne sanannen ɗan siyasa a Jihar Niger."

Etim ya ce:

"A matsayin shugaba, ba kai da addininka ba ne kawai. Kana wakiltar kowa, don haka dan adam ya fi addini muhimmanci."

Ojunekwu ya wallafa:

"Ko ta wane hanya zai kawo zaman lafiya a jiharsa, hakan abu ne mai kyau. Ina alfahari da Bago har yanzu."

Gwamna ya magantu kan alakarsa da mataimakinsa

A baya, kun ji cewa Gwamna Umaru Bago na jihar Niger ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da mataimakinsa, Yakubu Garba.

Gwamna Bago ya ce ba shi da wata matsala da Kwamred Yakubu Garba, manufofinsu ɗaya ne domin kawo ci gaba da gina sabuwar jihar Niger.

Ya bayyana cewa dangantakarsa da mataimakin gwamnan tana da kyau da armashi, inda ya buƙaci jama'a su yi watsi da jita-jita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.