‘Dan Arewa ya jawo abin alfahari, Farfesa Muhammad Pate Ya Zama Shugaban GAVI

‘Dan Arewa ya jawo abin alfahari, Farfesa Muhammad Pate Ya Zama Shugaban GAVI

  • Muhammad Ali Pate CON shi ne wanda zai zama sabon shugaban kungiyar GAVI a watan Agusta
  • Jose Manuel Barroso ya zabi Farfesa Pate a matsayin wanda zai hau kujerar Dr. Mr. Seth Berkley
  • Shekaru fiye da 20 da suka wuce aka kafa kungiyar ta GAVI domin a taimakawa kasashe da rigakafi

America - Mohammad Ali Pate wanda Farfesa ne a jami’ar Harvard a kasar Amurka, zai karbi ragamar kungiyar Gavi mai harkar allurar rigakafi.

A wani rahoto da ya zo a Vanguard, an fahimci Farfesa Mohammad Ali Pate zai zama sabon shugaban Gavi a ranar 3 ga watan Agusta mai zuwa.

Mohammad Ali Pate shi ne wanda zai maye gurbin Seth Berkley, wanda ya jagoranci kungiyar kiwon lafiyar na fiye da shekaru 10 tun daga 2011.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku Ya Fada Mani Zai Yi wa Nnamdi Kanu a Kwana 100 na Farko a Ofis - Wabara

Abin ban sha’awar shi ne baya ga jami’ar ta Harvard, Farfesa Pate ya yi aiki a babban bankin Duniya, kuma ya taba zama Ministan lafiya a gida.

Jose Manuel Barroso ya zabo Magajin Berkley

Rahoton ya ce jawabin da Gavi ta fitar a farkon makon nan, ya nuna asali Muhammad Pate kwararren likitan cututtuka masu yaduwa ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun tuni ake ta kokarin kawo wanda ya dace ya canji Berkley, sai aka yi dace da Farfesa Pate.

Farfesa Muhammad Ali Pate
Sabon shugaban GAVI, Muhammad Ali Pate Hoto: www.gavi.org
Asali: UGC

Shugaban majalisar da tayi aikin zakulo sabon shugaban Gavi, Jose Manuel Barroso ya ce a cikin wadanda suka nemi aikin, Farfesa Pate ya fita dabam.

Inda Farfesa Pate ya yi zarra

Tsohon shugaban kungiyar cigaban Turan ya ce sabon shugaban ya yi Ministan kiwon lafiya tsakanin shekarar 2011 da 2013 a gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Duk Da Buhari Na Tare Da Tinubu, Katsinawa Ba Za Su Zabe Shi Ba a 2023 - Toshon Shugaban NHIS

Pate ya rike Darektan kiwon lafiya na bankin Duniya daga 2019 zuwa 2021, shi ne ya jagoranci Dala biliyan $18bn da aka kashe wajen yaki da COVID-19.

The Cable ta ce malamin jami’ar ya nuna farin cikin karbar aikin wannan kungiya da aka kafa a 20000 domin taimakawa kasashe masu tasowa da rigakafi.

An haifi Pate mai shekaru 54 a karamar hukumar Misau a Bauchi, ya yi karatun likita a jami’ar ABU Zaria kafin tafiya kasar waje, mahaifinsa makiyayi ne.

Canjin kudin Najeriya a 1984

Kun ji labari Hassan Albadawi ya yi Kwamishina a gwamnatin Muhammadu Buhari, da ya zama Kantoma, Albadawi ya nemi alfarma da aka canza kudi.

Injiniya Buba Galadima ya ce saboda Albadawi ya roki Janar Buhari ya kara wa'adin canza kudi, aka sallami baffan na sa daga mukaminsa a 1984.

Asali: Legit.ng

Online view pixel