'Ku Ƙyale Shi': Ma'aikatar Lafiya Ta Dura kan Malamin Addini kan Hudubar Shan Gishiri

'Ku Ƙyale Shi': Ma'aikatar Lafiya Ta Dura kan Malamin Addini kan Hudubar Shan Gishiri

  • Ma’aikatar Lafiya ta yi watsi da ikirarin Fasto Chris Oyakhilome na cewa ana hana ‘yan Afrika amfani da gishiri don sayar da magunguna
  • Ta ce gishiri yana da amfani, amma yawan amfani da shi yana haddasa cututtuka kamar hauhawar jini, bugun zuciya da lalacewar koda
  • Ma’aikatar ta bukaci mutane su dogara da likitoci wajen samun shawarwari kan lafiya, ta kuma ce kimiyya da addini na iya aiki tare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Najeriya ta yi martani ga Fasto Chris Oyakhilome kan batun shan gishiri.

Fasto Chris Oyakhilome ya yi magana ne kan amfanin shan gishiri saɓanin masana lafiya da ke gargadi a kan yawan shansa.

Ma'aikatar lafiya ta yi wa Fasto martani
Ma'aikatar lafiya ta soki Fasto kan zancen gishiri. Hoto: Chris Oyakhilome.
Asali: Twitter

Shan gishiri: Ma'aikatar lafiya ta gargadi Fasto

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a jiya Laraba 7 ga watan Mayun 2025 a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatar tarayyar ta gargaɗi ‘yan ƙasa su guji yawan amfani da gishiri saboda kare lafiyarsu.

A kalamansa, Shugaban 'LoveWorld Incorporated (Christ Embassy)', Fasto Chris Oyakhilome, ya ce ana hana Afirka amfani da gishiri don a sayar da magunguna.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Ibukun Balogun, ya ce ko da yake sinadarin Sodium a cikin gishiri yana da amfani, ya kamata a rage amfani da shi.

Ya ce:

“Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta lura da wani faifan bidiyo da ya yadu wanda wani babban malamin addini ke ƙalubalantar shawarwarin likitoci.
“Muna girmama rawar da shugabannin addini ke takawa, amma dole ne mu gyara bayanan da ke barazana ga lafiyar jama’a.
“Gishiri ba matsala ba ne. Yana ɗauke da sodium, sinadari mai amfani ga jijiyoyi, motsi na tsoka, da daidaita ruwa a jiki.

Yawan gishirin da ya kamata a sha

Ma'aikatar lafiya ta yi karin haske kan yawan gishiri da ya kamata mutum ya sha da kuma illar rashin bin ka'ida.

Ta ce:

“Amma matsalar ita ce yawan amfani da shi. WHO da Gwamnatin Najeriya na ba da shawarar giram 5 kacal a kullum (kamar cokali ɗaya).
“Wuce wannan adadin na iya haddasa cututtukan da za a iya kaucewa kamar hawan jini, bugun zuciya, da ciwon koda.
“Bincike ya nuna cewa yawancin ‘yan Najeriya na cin fiye da sau biyu na adadin da aka yarda da shi.
An gargadi Fasto kan amfani da gishiri
Ma'aikatar ta gargadi Fasto game da amfani da gishiri. Hoto: Ministry of Health Nigeria.
Asali: Twitter

'Addini da kimiyya babu sabani' - Ma'aikatar lafiya

Ma’aikatar ta ƙara da cewa addini da kimiyya ba sa saba wa juna, kuma su na iya aiki tare don amfanin jama’a.

“A saboda haka, muna kira ga ‘yan ƙasa su nemi shawarwari daga likitoci kuma su mara wa ma’aikatar baya wajen rage cututtukan da za a iya kaucewa.”

- Cewar sanarwar

Fasto ya fadi sanadin mutuwar Fafaroma

A wani labarin, Fasto Chris Oyakhilome ya ce allurar rigakafin COVID-19 ce ta kashe Fafaroma Francis.

A cikin wani bidiyo, Oyakhilome ya soki Fafaroma saboda goyon bayan rigakafin, yana cewa lafiyarsa ta tabarbare bayan karɓar allurar.

Faston ya ce shanyewar jiki da ta yi sanadin mutuwar Fafaroma ta samo asali ne daga toshewar jini da allurar rigakafin ke haddasawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.