'Yan APC Sun Fallasa Masu Neman Hukumar EFCC Ta Binciki Matawalle
- Ƙungiyar matasan APC ta AYLCN ta nuna yatsa ga masu yin zanga-zangar neman hukumar EFCC ta binciki Bello Matawalle
- Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa wasu ƴan siyasa suke ɗaukar nauyin masu zanga-zangar don cimma wasu muradunsu
- An ji cewa Olayemi Isaac ya buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa lura sosai da zarge-zargen da ake yaɗawa ba tare da wata hujja ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar APC Youth Leaders Network (AYLCN) ta yi magana kan zanga-zangar da aka yi don neman hukumar EFCC ta binciki Bello Matawalle.
Ƙungiyar AYLCN ta nesanta kanta daga zanga-zangar da aka gudanar kwanan nan wadda ke neman gudanar bincike kan ƙaramin ministan tsaron.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar AYLCN, Olayemi Isaac, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An buƙaci EFCC ta binciki Bello Matawalle
A ranar Juma’a ne wasu da ke kiran kansu ƙungiyar APC-YLA suka gudanar da zanga-zanga a hedikwatar EFCC da ke Abuja, inda suka buƙaci a ci gaba da binciken zargin cin hanci da ake yi wa Matawalle lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara.
Kungiyar ta zargi EFCC da yin shiru kan shari’ar duk da korafe-korafen da aka shigar da kuma alkawarin da hukumar ta yi a baya na yin bincike.
Su waye ke ɗaukar nauyin masu zanga-zangar?
Olayemi Isaac ya bayyana cewa wannan zanga-zangar da aka yi, wasu ƴan siyasa ne daga jihar Zamfara suka ɗauki nauyinta, rahoton The Nation ya tabbatar.
“A bayyane yake cewa abubuwan da suka faru kwanan nan, na zanga-zanga a EFCC ta hannun wata kungiya da ta bayyana kanta a matsayin matasan APC, wacce ta sayar da mutuncinta, wani ƙoƙari ne na yaɗa ƙarya."
“Lalle ne a wannan lokaci mai sarkakiya ana buƙatar ƴan Najeriya su yi karatun ta natsu kan duk wani zargi da ake yaɗawa ba tare da hujja ba."
“Duk da haka, jajircewarmu ga gaskiya, adalci, da kare martabar dimokuraɗiyya da jam’iyyar APC ke tsayawa a kai ba za ta gushe ba."
“A bayyana yake Bello Matawalle ɗan ƙasa ne nagari wanda gudunmawarsa ga harkar tsaron ƙasa, musamman a yankin Arewa maso Yamma, na ci gaba da tallafawa hangen nesa na manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu."
- Olayemi Isaac

Asali: Facebook
Olayemi Isaac ya ƙara da cewa maimakon ƴan siyasa su ɗauki nauyin zanga-zanga don biyan buƙatunsu, ya kamata su mai da hankali wajen magance taɓarɓarewar tsaro a jiharsu.
Bello Matawalle ya ba da tallafin N5m
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ba da tallafi ga iyalan limamin da ƴan bindiga suka kashe a Zamfara.
Matawalle ya ba iyalan marigayi Alkali Salihu Sulaiman tallafin N5m da buhun shinkafa 10 bayan ya kai ziyarar ta'aziyya a gidansa.
Ministan tsaron ya nuna damuwa kan yadda ƴan bindiga ke addabar malaman addini da hare-hare a jihar Zamfara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng