NDLEA ta Bankado Wata Tafkekiyar Gonar Wiwi a Jihar Kano

NDLEA ta Bankado Wata Tafkekiyar Gonar Wiwi a Jihar Kano

- Hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano ta gano katuwar gonar wiwi a jihar

- Shugaban hukumar na jihar Kano, Malam Isah Limita ya tabbatar da gano gonar da suka yi a garin Gwarzo

- Ya bukaci jama'a da su taimakawa hukumar da bayanan sirri ta yadda zasu kama tare da hukunta masu laifi

Shugaban hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano, Malam Isah Limita Muhammad yace hukumar ta bankado wata tafkekiyar gonar wiwi a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.

Shugaban hukumar ya sanar da manema labarai hakan a jiya a garin Kano. Ya ce, "Yanzu muka bankado wata tafkekiyar gonar wiwi a Gwarzo kuma mun cafke mamallakinta. Za mu gurfanar dashi a gaban shari'a nan babu dadewa.

"Hakazalika, an sanar damu wata gonar a wani wuri na daban amma har yanzu bamu gano ta ba. Bayan mun kammala bincike za mu gurfanar da masu ita domin su fuskanci fushin shari'a."

KU KARANTA: Fani Kayode ya musanta cin zarafin ma'aikatansa na cikin gidansa, ya garzaya gaban kotu

NDLEA ta Bankado Wata Tafkekiyar Gonar Wiwi a Jihar Kano
NDLEA ta Bankado Wata Tafkekiyar Gonar Wiwi a Jihar Kano. Hoto daga @Leadership
Asali: Twitter

KU KARANTA: Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi hakan

A yayin da aka tambaye shi kan yadda wasu ma'aikatan hukumar ke daga wa wasu kafa, shugaban yace lamarin na cikin gida ne amma ana bincike domin hukunta duk wanda aka kama da hakan.

Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa, Mohammed yayi kira ga jama'a da su baiwa hukumar goyon baya ta hanyar basu bayanan da zasu taimaka musu wurin yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi.

A wani labari na daban, shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya, Lucky Irabor, ya baiwa ƴan Najeriya tabbacin yin aiki tuƙuru don basu kariya.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin a Abuja yayin jawabi a wani taron jami'an tsaro mai taken "Cigaban bunkasa ayyukan samar da tsaro da ta'addanci a Najeriya".

A cewarsa, jami'an tsaron Najeriya a tsaye suke, tsayin-daka domin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan musamman ganin halin rashin tsaro, ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran matsalolin da suka addabi kasa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel