NDLEA Ta Gano Katafaren Gonar Da Ake Noman Wiwi a Sokoto, Ta Cafke Mutum Daya

NDLEA Ta Gano Katafaren Gonar Da Ake Noman Wiwi a Sokoto, Ta Cafke Mutum Daya

Jihar Sokoto - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, shiyyar Jihar Sokoto, ranar Juma'a, ta kama wani Anas Sani, mai shekaru 32, wanda aka gano yana noman tabar wiwi a jihar.

Babban Kwamandan Hukumar a jihar, Iro Adamu, a bayaninsa, ya ce sun gano haka ne a binciken da aka gudanar daren Juma'ar da ta gabata a yankin Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar, bayan samun bayanan sirri.

An kama wani Anas Sani da ake zargin manomin wiwi ne a Sokoto.
Jami'an NDLEA sun kama wani dan shekara 32 da ake zargin manomin wiwi ne a Sokoto. Hoto: New Telegraph
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An shuka tabar ne a gonar masara ta yadda iya kwararru ne kawai za su iya gane menene.
"Ta waje ce mai karfi kuma mai tsada," in ji shi.

Adamu ya ce wannan ne karon farko da aka samu irin gonar a jihar, wanda ya ce, dole a gudanar da gangamin yawan wayar da kai don dakike al'umma daga fadawa haramtattun kasuwanci.

Kara karanta wannan

“Idan ba’a kira ni dan midiya ba ɗan uwarki za’a kira ni” Na hannun daman Ganduje ya wanke budurwa

Wanda ake zargin, mai 'ya'ya biyu, da yake zantawa da manema labarai, ya ce ya koyi kasuwancin a Jihar Lagos lokacin da ya ke sana'ar kanti.

"Wannan ne karo na farko. Na koya lokacin ina rayuwa a Lagos sai na yanke shawarar yi a garinmu Sayinna.
"Babban yayana yayi bakin kokari kar na yi amma banji shawara ba.
"Nagode Allah da aka kama ni kafin in fara cin riba.
"A shirye nake na karbi hukuncin abin da na aikata saboda ya zama izna ga masu sha'awa nan gaba," in ji shi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164