Gwamnatin Tinubu Ta Sanar da Adadin Musulmin da Za Su Yi Hajjin Bana, Jigin Farko Ya Tashi

Gwamnatin Tinubu Ta Sanar da Adadin Musulmin da Za Su Yi Hajjin Bana, Jigin Farko Ya Tashi

  • Gwamnatin Tarayya ta ce musulmi 64,188 daga Najeriya ne za su sauke farali a aikin hajjin bana 2025
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a wurin kaddamar da fara jigilar maniyyatan a jihar Imo
  • Shettima ya ja hankalin maniyyatan da su tuna su jakadun Najeriya ne a ƙasa mai tsarki, don haka su rike mutuncinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Imo - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ƴan Nigeriya 64,188 ne za su sauke farali a aikin hajjin bana 2025 a ƙasar Saudiyya.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya sanar da hakan ranar Juma’a yayin ƙaddamar da fara jigilar mahajjata zuwa ƙasa mai tsarki.

Maniyyatan Najeriya.
Musulmai ƴan Najeriya sama da 64,000 za su sauke farali a hajjin bana 2025 Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Hakan na kunshe a wata sanarwa da Sanata Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Tuwita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin mahajjata na farko ya tashi a Imo

Jirgin farko ya kwashi maniyyata daga filin jirgin sama na Sam Mbakwe International Cargo Airport da ke Owerri, jihar Imo.

Wannan na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da filin jirgin ya samu, saboda wannan ne karo na farko da jirgin ƙasa da ƙasa ya tashi daga filin.

Shettima ya yaba wa Gwamna Hope Uzodimma bisa ƙoƙarin da yake yi wajen haɗin kai da juriya tsakanin addinai a jihar Imo.

“Ina yaba wa Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, saboda yadda ya karfafa zaman lafiya da mutunta juna tsakanin mabiya addinai. Wannan al’amari yana da muhimmanci matuƙa ga daidaiton Najeriya,” in ji Shettima.

Tinubu ya tura sakon fatan alheri ga mahajjata

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma isar da saƙon fatan alheri daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga mahajjatan.

Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya samar da duk ababen da ake bukata domin nasarar aikin hajjin bana.

Shettima ya ce:

“Shugaban Ƙasa, kamar yadda aka san shi da hangen nesa, ya samar da duk kayan aiki da kuɗin da suka wajaba domin ganin an yi nasara a hajjin shekarar 2025."

Gwamnatin Tinubu ta yi wa mahajjata nasiha

Ya kuma gargadi mahajjata da kada su manta da nauyin da ke wuyansu na kasancewa jakadun Najeriya a ƙasar waje.

“Mahajjata ku sani cewa ba kun je kawai don ibada ba ne, ku jakadu ne na ƙasarmu. Ku riƙe mutuncin tutar Najeriya. Kowane hali da za ku nuna yana wakiltarmu ne gaba ɗaya..”

Shettima ya kuma ja kunnen jami’an kula da jigilar mahajjatan da su dauki aikinsu a matsayin amana daga Allah, su guji kura-kurai kamar na shekarun baya.

A ƙarshe, ya yaba da kokarin hukumar NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki da suka yi aiki tukuru don ganin cewa aikin hajjin 2025 ya samu nasara.

Za a fara jigilar mahajjata a jihar Kwara

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar jin daɗin alhazai ta Kwara ta bayyana cewa za a fara jigilar alhazan jihar daga filin jirgin sama na Ilorin zuwa Saudiyya ranar 12 ga Mayu.

Hukumar ta ƙara da cewa rukuni na biyu za su tashi ranar 14 ga Mayu, rukuni na uku kuma za su tafi Saudiyya a ranar 16 ga Mayu, sannan na karshe kuma ranar 17 ga Mayu.

Shugaban hukumar jin daɗin alhazan Kwara, Abdulsalam Abdulkadir ne ya yi wannan bayani a taron wayar da kan maniyyata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262