Mutumin Da Ya Fara Karatun Boko a Najeriya: Muhimman Abubuwa 4 Game Da Olaudah Equiano

Mutumin Da Ya Fara Karatun Boko a Najeriya: Muhimman Abubuwa 4 Game Da Olaudah Equiano

A kowane abu a rayuwa, akwai mutum na farko ko mutane na farko da suka fara yinsa kuma akan samu hakan a dukkan bangarori na rayuwa.

Masana tarihi sun tattaro bayanai da sauran abubuwa masu ban sha’awa dangane da Olaudah Equiano, mutum na farko da ya fara karatun boko a Najeriya.

An fara ilimin boko a Najeriya a shekarar 1842 sai dai a tarihi shi ne mutum na farko da ya fara tara ilimin boko a kasar nan.

Muhimman Abubuwa 4 Game Da Olaudah Equiano, Mutumin Da Ya Fara Karatun Boko a Najeriya
Olaudah Equiano, mutumin da ka ce shi ya fara karatun Boko a Najeriya. Photo Credit: Motivation.africa, The British Library, Wealth Result
Asali: Facebook

Kamar yadda Wealth Result ta ruwaito, Olaudah Equiano ba shi ne mutum na farko da ya fara karatun ba, sai dai shi ne mutum na farko da ya fara rubutun littafai a Najeriya.

Legit.ng ta tattaro abubuwa 4 da ya kamata a sani akan sa:

Kara karanta wannan

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tashi cikin dare ya fara tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. An haife shi a Essaka, Eboe wanda yanzu yankin kudu maso gabashin Najeriya ne

Wikipedia ta bayyana yadda ka haife Olaudah Equiano a Essaka, Eboe a shekarar 1745 a masarautar Benin. Kauyen sa yanzu a kudu maso gabashin Najeriya ya ke.

A tarihin sa, shi ne auta a cikin yaran mahaifin sa, gidan su akwai yara maza 6 da mace daya.

2. An yi garkuwa da shi ya na da shekaru 11 sannan aka sayar da shi a matsayin bawa

Ya fara wahalar rayuwa ne tun bayan da aka yi garkuwa da shi lokacin ya na da shekaru 11.

Wealth Result ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da Equiano da kanwar sa daga nan turawa su ka siye su, daga nan aka dinga yawo da su wuri-wuri.

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

An ruwaito yadda shi da sauran mutane 244 ‘yan Afirka da aka ketare tekun Atlantic zuwa Barbados kafin a mayar da su Turai.

3. Ya samu ‘yancin kan sa a 1766

Olaudah Equiano ya fanshi kan sa a 1766 daga ubangidan sa, Robert King. Ya fanshi kan sa da 40 pounds, a shekarar 2019 kimar kudin ta kai N3,119,258.

Bayan ya samu ‘yan cin kan sa ya yi kokarin tserewa kawai wasu su ka kara kama shi aka shigar da shi wani jirgin ruwa a Georgia. A shekarar 1768 ne ya koma Ingila inda ya ci gaba da aiki a rafi.

4. Ya na cikin wadanda su ka tsaya tsayin-daka wurin dakatar da sayar da bayi

A shekarar 1783 ne ya fara taimakon bakaken fata ma su karamin karfi na birnin London, wadanda yawancin su masu jinin Afirka da Amurka ne a hade, bayan sun samu ‘yancin kai daga Turawa su ka ci gaba da rayuwa a can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel