Gwamna Ya ba Mutane Mamaki a Wani Faifan Bidiyo, Ya Tuna Lokacin da Yake Koyarwa

Gwamna Ya ba Mutane Mamaki a Wani Faifan Bidiyo, Ya Tuna Lokacin da Yake Koyarwa

  • Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya ba mutane da dama mamki yayin da ya shiga aji kuma ya koyar da ɗalibai a makaranta
  • A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Aiyedatiwa na tambayar ɗalibai nau'ikan magunguna
  • Mai girma Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta inganta harkokin ilimi a Ondo ta yadda za a goga da ɗalibai a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - A wani faifan bidiyo mai taɓa zuciya da ya karade kafafen sada zumunta a ranar Juma’a, an ga Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya na koyarwa a aji.

Faifan bidiyon ya nuna Gwamna Aiyedatiwa yana koyarwa a wani aji da ke wata makaranta da ba a bayyana sunanta ba.

Gwamna Aiyedatiwa.
Gwamna Aiyedatiwa ya koma aji, ya koyar ɗalibai a jihar Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

An wallafa bidiyon a shafin Gwamna Lucky Aiyedatiwa na Facebook tare da taken, "Malamin makaranta malami ne a kowane lokaci."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamna ya koyar da ɗalibai a Ondo

A cikin bidiyon an ga Gwamna Aiyedatiwa ya rubuta kalmar "Drugs" watau magunguna a kan allo yana kuma tambayar ɗalibai su faɗi nau’ikan magunguna.

Gwamna ya nuna farin ciki da gamsuwa yadda ya ga ɗaliban suna ba shi amsoshin tambayar da ya yi masu.

Za a ɗauki malaman makaranta a Ondo

Wannan lamari na zuwa ne makonni bayan gwamnan ya amince da daukar sababbin malamai 1,100 domin koyarwa a makarantun firamare a fadin ƙananan hukumomi 18 na jihar Ondo.

A cewar Aiyedatiwa, shirin ɗaukar malaman, wanda ya samu tallafin hadin gwiwa tsakanin hukumomin UBEC da SUBEB na 2023/2024, yana daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin inganta harkokin ilimi.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Gwamnan Ondo ya faɗi nasaorin da ya samu a ɓangaren ilimi Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Nasarorin da gwamnan Ondo ya samu

A wani karin bayani da ya wallafa tare da bidiyon, gwamnan ya bayyana wasu muhimman nasarori da aka samu a fannin ilimi da suka haɗa da:

  • Raba littattafai, wayoyin hannu na zamani (Android tablets), da kayan wasanni ga makarantun gwamnati.
  • Ginawa da gyaran azuzuwa a makarantu sama da 100
  • Raba sama da littattafai 75,000 da kayan koyo na zamani
  • Daukar malamai 2,100 da horar da su sanin makamar aiki
  • Inganta harkokin wasannin yara a makarantu don ƙara hazaƙar ɗalibai.

Aiyedatiwa ya ce:

“Muna gina tubalin cigaba mai ƙarfi ga ƙarni na gaba, za mu tabbatar da cewa yaranmu sun samu kwarewar da ake buƙata don cin nasara a zamanin da muke ciki da ke ƙara sauyawa."

Gwamnan Ondo ya biya wa ɗalibai kudin WAEC

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya amince da fitar da kudi sama da Naira miliyan 600 domin biya wa ƴaƴan talakawa kuɗin jarabawar WAEC.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Ebenezer Adeniyan, ya fitar, gwamnan ya biya wa ɗaliban da ke karatu a makarantun sakandiren gwamnatin kuɗin WAEC ta 2024/2025.

Rahoto ya nuna cewa matakin zai bai wa dalibai 23,048 da suka ci jarabawar karin girma ta JSS II damar yin rajista domin zana jarabawar WASSCE ta bana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262