Gwamna Ya Ayyana Juma'a a Matsayin Ranar Hutu, PDP Ta Fasa Shiga Zaben Ciyamomi
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ayyana Juma’a, 17 ga Janairu, a matsayin ranar hutu domin bai wa mazauna Ondo damar yin zaben ciyamomi
- Rundunar 'yan sanda ta hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa a ranar Asabar daga karfe 6:00 na safe zuwa 4:00 na yamma
- Sai dai jam'iyyar PDP ta sanar da janyewarta daga zaben kananan hukumomin saboda rashin amincewa da tsarin hukumar zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ayyana Juma’a, 17 ga Janairu, a matsayin ranar hutu don zaben kananan hukumomi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ondo (ODIEC) ta tsara gudanar da zaben ciyamomin ne a ranar Asabar, 18 ga watan Janairu.

Asali: Facebook
Ondo: Gwamna ya ayyana ranar hutu
The Nation ta rahoto babban sakataren yada labaran gwamnan, Ebenezer Adeniyan, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 16 ga Janairu, 2025.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa an dauki matakin ba da hutun don bai wa mazauna jihar damar kada kuri'unsu a zaben kananan hukumomin.
“Gwamnatin jihar Ondo ta ayyana Juma’a, 17 ga Janairu, 2025, a matsayin ranar hutu ga ma’aikata don ba su damar yin zabe.”
“Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya bukaci kowa ya ba da gudunmawa don ganin zaben kananan hukumomin ya gudana cikin lumana."
- A cewar sanarwar.
PDP ta fasa shiga zaben ciyamomin Ondo
Jam’iyyar PDP reshen jihar ta bayyana rashin gamsuwa da tsarin zaben da hukumar ODIEC ke gudanarwa a jihar, don haka ta sanar da ficewa daga zaben ciyamomin.
Leye Igbabo, daraktan yada labarai na PDP, ya ce sun fasa shiga zaben kananan hukumomin ne saboda rashin amincewa da ingancin tsarin zaben.
Igbabo ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar janyewa bayan shawarwari da shugabanni da sashen gudanarwar jam’iyyar a kasa.
Shi ma mukaddashin shugaban PDP a jihar, Bakita Bello, ya bayyana janyewar jam’iyyar ga manema labarai a Akure a ranar Alhamis, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
An sanya lokacin da maniyyata za su kammala biyan kudin Hajjin 2025 a jihar Kwara
Bello ya ce jam’iyyar ta rasa kwarin gwiwa a kan ikon hukumar zabe wajen gudanar da zabe mai adalci.
Hukumar Zabe ta yi wa PDP martani
Hukumar zaben jihar, ODIEC ta tabbatar da cewa ficewar PDP daga zaben ba zai kawo cikas ga tsarin zaben da ta shirya ba.
ODIEC ta ce fiye da jam’iyyun siyasa 10 ne za su shiga wannan zaben da aka shirya don haka janyewar PDP ba zai dakatar da shirinta ba.
'Yan sanda sun takaita zirga-zirga a Ondo
A wani bangare, rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar da hana zirga-zirgar ababen hawa da babura daga karfe 6:00 na safe zuwa 4:00 na yamma ranar Asabar, inji rahoton Punch.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Wilfred Afolabi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Akure, ta hannun kakakin rundunar, CSP Funmilayo Odunlami, ya ce an dauki matakin ne saboda dalilai na tsaro.
INEC ta ayyana wanda ya lashe zaben Ondo

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC a zaben Ondo da aka gudanar a ranar 17 ga Nuwamba, 2024.
Aiyedatiwa ya samu kuri'u 366,781, yayin da dan takarar PDP, Ajayi Agboola, ya samu kuri'u 117,845, kamar yadda baturen zabe, Farfesa Olayemi Akinwunmi, ya bayyana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng