"Ba Za Su Iya ba": Gwamna Ya Sallami Hadimai 2 Mata daga Aiki, Ya Umarci Su Bar Ofis

"Ba Za Su Iya ba": Gwamna Ya Sallami Hadimai 2 Mata daga Aiki, Ya Umarci Su Bar Ofis

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi garambawul a tawagar yaɗa labaransa, ya kori hadimai biyu duk mata daga aiki
  • Mai magana da yawun gwamnan, Ebenezer Adeniyan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Akure, babban birnin jihar Ondo
  • Ya kuma.umarci waɗanda aka sallama daga aiki su miƙa dukkan kayayyakin da ke hannunsu ga shugaban ma'aikatan fadar gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya sallami mata biyu daga cikin hadimai masu taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a.

Gwamna Aiyedatiwa ya ɗauƙi wannan matakin ne domin inganta ayyukan gwamnatinsa musamman a ɓangaren hulda da jama'a.

Gwamna Aiyedatiwa.
Gwamnan Ondo ya sallami hadimai 2 daga aiki Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Mai magana da yawun gwamnan, Ebenezer Adeniyan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Akure, babban birnin Ondo, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimai 2 mata da gwamnan ya kora

Waɗanda korar ta shafa sun haɗa da babbar mataimakiya ta musamman kan bincike da rubuce-rubuce, Ewatomilola Emiola.

Sannan akwai mai taimaka wa gwamnan kan harkokin kafafen sada zuminta, Kikelomo Isijola.

Wannan mataki ya biyo bayan yunkurin gwamnan na sake fasalin tawagar hulɗa da jama’a ta fadar Gwamnatin Jihar Ondo.

Sanarwar ta bayyana cewa sallamar wadannan hadamai guda biyu na da nufin ƙara inganta tsare-tsaren sadarwa a gwamnatin jihar, rahoton New Telegraph.

Bincike ya nuna cewa ana iya samun wasu sauye-sauye a tawagar yaɗa labaran gwamnan a nan gaba, domin ƙara inganta manufofin gwamnatinsa.

Ya umarci hadiman su ajiye kayan gwamnati

Gwamna Aiyedtaiwa ya umarci hadiman da aka sallama da su gaggauta miƙa duk wasu kayayyakin gwamnati da ke hannunsu ga ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.

Lucky Aiyedatiwa ya gode wa tsofaffin hadiman biyu bisa gudummawar da suka bayar a gwamnatinsa, yana mai yi musu fatan alheri a rayuwarsu ta gaba.

"An umarci waɗanda matakin korar ya shafa su miƙa dukkan kayan da ke hannun ga shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Odo.
"Mai girma gwamnan ya gode masu tare da fatan alheri a dukkan ayyukan da za su sa a gaba," in ji Ebenezer Adeniyan.

Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma, inda wasu ke kallonsa a matsayin yunkuri na gyara, yayin da wasu ke ganin hakan na da nasaba da siyasa.

Gwamnan Ondo ya rusa majalisar zartarwa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwa a shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati bayan lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo.

Wannan mataki ya shafi dukkan mambobin majalisar ban da mutum biyu da suka hada da kwamishinan shari’a, Dr Kayode Ajulo, da kwamishinar kudi, Omowunmi Isaac.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262