Rikicin LP: Gwamna Ya Maida Zazzafan Martani bayan Jam'iyya Ta Dakatar da Shi

Rikicin LP: Gwamna Ya Maida Zazzafan Martani bayan Jam'iyya Ta Dakatar da Shi

  • Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi fatali da dakatarwar da tsagin jam'iyyar LP karkashin jagorancin Julius Abure ya yi masa
  • Alex Otti ya bayyana cewa hukuncin kotun koli ya cire Abure daga matsayin shugaban LP, don haka ba shi ikon ɗaukar wannan matakin
  • Tun farko dai LP karkashin jagorancin Abure ta sanar da dakatar da Gwamna Otti da ƴan Majalisar Tarayya biyar bisa zargin cin amanar jam'iyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Gwamnan Jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya bayyana dakatarwar da tsagin LP karkashin Julius Abure ya masa a matsayin abin dariya.

Gwamna Otti ya yi ikirarin cewa Abure ya ɗauki wannan matakin ne domin neman suna da jawo hankali jama'a.

Abure da Gwamna Otti.
Gwamnan Abia ya yi fatali da dakatarwar da tsagin Abure ya yi masa Hoto: @LabourNG
Asali: Twitter

Punch ta ce Otti ya faɗi hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mr. Ferdinand Ekeoma, ya fitar a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko dai LP karkashin jagorancin Abure ta sanar da dakatar da Gwamna Otti, sanatoci biyu da ƴan Majalisar Wakilai 3 bisa zargin cin amanar jam'iyya.

Gwamna Alex Otti ya caccaki Julius Abure

Da yake martani a sanarwar, Otti ya ce kotun koli ta riga ta yanke hukunci cewa Julius Abure ba shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar LP ba.

Bisa haka, gwamnan ya ce ya kamata hukumar ’yan sanda ta kama shi bisa laifin sojan gona da karyar mukami, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Alex Otti ya kara da cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta watau INEC ta karbi hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na tsige Abure saboda wa'adinsa ya kare.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Wannan sanarwar da Abure da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa suka fitar rashin mutunta dimokuraɗiyya ne, da amfani da sunan Gwamna Otti don biyan buƙatunsu na son zuciya.”

Kotun koli ta tsige Abure daga shugabancin LP

Gwamna Otti ya ce hukuncin kotun koli ya bayyana a fili cewa wa'adin Abure ya ƙare kuma ba shi da ikon ci gaba da kiran kansa shugaban jam’iyyar LP.

A cewarsa, hakan ne ya sa masu ruwa da tsakin LP suka kafa kwamitin rikom ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Sanata Nenadi Usman.

Alex Otti ya kara da cewa Abure ya dakatar da shi ne bayan shugabannin LP sun aika masa da takardar gayyata domin ya zo ya kare kansa kan zarge-zargen almundahana da karya dokokin jam'iyya.

Ya ce duk shure-shuren da Julius Abure yake yi ba zai hana shi mutuwa ba, kuma yana yin haka ne domin neman suna da ɗauke hankali kan zarge zargen da ke masa.

Gwamna Alex Otti.
Gwamna Otti ya buƙaci ƴan Najeriya su yi watsi da sanarwar Abure Hoto: Alex C. Otti
Asali: Facebook

Gwamnan Abia ya aika saƙo ga ƴan Najeriya

Gwamna Otti ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su dauki wannan sanarwa ta Abure da muhimmanci, yana mai cewa:

“Abure da abokan harkallarsa wasu mutane ne da ke ƙoƙarin karɓar rawanin da ba su cancanci sawa ba.”

Gwamna Otti ya jawo jiga-jigai zuwa LP

A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar dokokin Abia mai wakiltar Isuikwuato, Lucky Johnson (PDP) da magabacinsa, Chukwudi Ogele sun koma LP a Abia.

Manyan jiga-jigan siyasar sun fice daga PDP zuwa jam'iyya LP ne saboda ayyukaan ci gaba da Gwamna Alex Otti ke yi wa al'umma.

Gwamna Otti ya yaba da matakin masu sauya shekar, yana mai cewa sun zabi gaskiya kuma sun rungumi haske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262