Dandazon Mata Fiye da 1,000 Sun Fito Zanga-Zanga Zigidir a Anambra

Dandazon Mata Fiye da 1,000 Sun Fito Zanga-Zanga Zigidir a Anambra

  • A wani abu da ya ja hankulan mutane, an rahoto mata na yin zanga-zanga tsirara a jihar Anambra kan kashe-kashe da ya addabi garin Awka
  • Masu zanga-zangar sun karade babban birnin jihar dauke da kwalaye da ke nuni da batancin ransu kan cin hanci da rashawa da ya mamaye 'yan sandan jihar
  • Sun bukaci hukumar 'yan sanda da ta sallami wasu jami'anta da suke da hannu a rashawa, da kuma kawo karshen kashe mutanen su da matsafa ke yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Awka, jihar Anambra - Akalla mata 1,000 daga kauyuka 20 a karamar hukumar Awka ta Kudu, jihar Anambra suka fito kan tituna tsirara suna zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, inda rahotanni suka bayyana cewa, matan na zanga-zangar ne kan kashe-kashen da ake yi a garuruwansu.

Mata sun fito tsirara suna zanga-zanga a Anambra
Duk da suna tsirara ba su damu ba, haka suka karade babban birnin jihar suna rokon a kawo karshe kashe mutanensu da matsafa ke yi Hoto: Nigerian Police
Asali: Facebook

Masu zanga-zangar sun bukaci a kori wasu jami'an 'yan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da suna tsirara ba su damu ba, haka suka karade babban birnin jihar dauke da kwalaye masu rubutu, suna zargin wasu jami'an 'yan sanda da hannu a cin hanci da rashawa, rahoton da jaridar The Nation ta fitar.

An gansu dauke da akwatin gawa da ke nuna alamar binne jami'an 'yan sandan da suke zargi, tare da ba hukumar wa'adin kwanaki 7 ta kori jami'an.

An rubuta a jikin wasu kwalayen cewa: "Matsafa na kashe mutanen mu", "A kori bara gurbi a aikin 'yan sanda", “DC na haifar da matsalar tsaro a Awuka”, “A kawo karshen cin hanci da rashawa”, da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir, APC sun ja layi kan zanga-zangar da aka gudanar bayan fitar da takardun CTC

Ko mecece manufar yin zanga-zangar?

Da yake magana a madadin masu zanga-zangar, Richard Onuorah, ya ce daga yanzu jama'arsu ba za su amince da kashe-kashe da nakasa mutanensu ba.

Shima da yake jawabi, shugaban kungiyar garin na Ezinano, Tochukwu Nwokoye, ya bayyana fatansa na cewa zanga-zangar zata kawo karshen tashe tashen hankula a Awka.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa tun a watan Satumba matan suka yi barazanar yin zanga-zangar tsirara ma damar ba a daina kashe mutanensu ba.

Matan aure sunyi zanga-zanga kan tsadar abinci a Kaduna

A wani labarin, wasu matan aure a karamar hukumar Igabi sun yi zanga-zangar lumana don nuna damuwa kan halin da ake ciki, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Matan su ka ce sun fito ne don rokon Shugaba Tinubu ya yi wani abu don kawo karshen tsadar abinci da yunwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel