'Aso Rock Ta Birkice,' Atiku Ya Mayar da Martani ga Fadar Shugaban Kasa

'Aso Rock Ta Birkice,' Atiku Ya Mayar da Martani ga Fadar Shugaban Kasa

  • Ofishin yada labaran Atiku Abubakar ya caccaki Daniel Bwala bisa sukar Wazirin Adamawa, ya ce kalamansa na cike da rufa-rufa da son zuciya
  • Sanarwar ta ce jam’iyyar APC na jin tsoron hadakar siyasa da Atiku ke jagoranta tare da wasu shugabannin hamayya domin ceto Najeriya
  • Ofishin Atiku ya bayyana shi a matsayin jigo a siyasar adawa tun 1999, yana mai cewa duk wata kima da Bwala ke da ita ta samo asali daga Atiku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ofishin yada labarai na tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan kalaman hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala.

A wata sanarwa da ofishin Atiku ya fitar ranar Talata, an caccaki Bwala bisa kalamansa na cewa kila Ubangiji bai kaddarawa tsohon ubangidansa shugabantar Najeriya ba.

Atiku
Ofishin yada labaran Atiku ya caccaki fadar shugaban kasa Hoto: Daniel Bwala/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa Bwala, wanda ya kasance kakakin yakin neman zaben Atiku a 2023 kafin ya koma APC mai mulki, ya zargi Atiku da kin yin murabus daga siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata Atiku ya ajiye duk wani abu da ya shafi sake neman takara a zaben kasar nan.

Atiku ya caccaki hadimin Tinubu

Daily Post ta ruwaito Masu magana da yawun Atiku sun ce kalaman Bwala da na wasu hadiman Tinubu na nuna yadda APC ke tsoron hadakar ‘yan adawa.

Sanarwar ta ce:

"Abin dariya ne kuma abin tausayi yadda Bwala, wanda ya canja sheka ke nusar da Atiku a kan makomarsa."
“Kalamansa cike suke da rashin da'a da son zuciya, alamar cewa yana neman karbuwa cikin sahun gwamnati mai ci da ke tangal-tangal.”

Ana ganin hadakar Atiku na kara karfi

A cewar ofishin yada labaran Atiku, hadakar da ake kokarin ginawa na da nufin kwato Najeriya daga tabarbarewar tattalin arziki, gazawar hukumomi, da raunin dimokiradiyya.”

Sanarwar ta kara da cewa:

"Atiku Abubakar shi ne mutum mafi karfi a cikin ‘yan adawa a Najeriya, kuma hadakar da yake ginawa na barazana kai tsaye ga tsarin jam’iyyar da ke mulki."
Bwala
Ofishin yada labaran Atiku ya ce tarayyar Bwala da tsohon dan takarar PDP ne ya daga shi a siyasa Hoto: Bwala
Asali: Twitter

A jawabin, an kare siyasar Atiku, inda aka bayyana shi a matsayin gwarzon tabbatar da sauyi tun bayan dawo da mulkin farar hula a 1999.

Sanarwar ta kuma ragargaza Bwala, tana mai cewa duk wata kima da yake da ita yanzu ta samo asali ne daga kasancewarsa tare da Atiku a baya.

Atiku ya yi magana kan barin PDP

A baya, mun wallafa cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa daga jita-jitar cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyarsa.

Wazirin Adamawa ya ce yana nan daram a PDP tare da jaddada cewa haɗakar da yake jagoranta za ta kasance makamin kawar da gwamnatin APC a zaɓen 2027 mai zuwa.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar mata 'yan majalisar amintattu ta PDP, ƙarƙashin jagorancin tsohuwar ministar harkokin mata, Hajia Inna Ciroma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.