Wata Hamshakiyar Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m

Wata Hamshakiyar Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m

  • Wata Mai kuɗi dake zaune a Birnin tarayya Abuja ta shiga neman kyakkyawan Saurayin da zai iya ɗirka mata ciki
  • Attajirar ta yi alkawari baiwa duk wanda iya wannan aiki kuɗi naira Miliyan Uku amma akwai sharuddan da ta kafa
  • Bayan rufe wa mutumin fuska a duk lokacin da zai sadu da ita, tace zata kulle shi a gida har sai lokacin da aka tabbatar ta samu juna biyu

Abuja - Wata mazauniyar burnin tarayya Abuje dake faɗi tashin zama uwa tana neman kyakkyawan mutumin da zai iya sanya wa ta ɗauki ciki.

Tauraruwar mai amfani da kafar sada zumunta, Uwaoma Susan Joseph, ita ce ta bayyana bukatar matar a dandalin Facebook tare da sakaya bayanan matar.

Wata mata a Abuja.
Wata Hamshakiyar Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m
Asali: Getty Images

Akwai kyautar miliyan N3m ga mutumin

Yayin da matar mai kuɗi ta shirya biyan duƙ wanda ya ci sa'ar gama wannan aikin Naira Miliyan N3m, ta kuma kafa wasu sharuɗɗa yayin gudanar da lamarin.

Kara karanta wannan

Atiku Ko Tinubu? Daga Karshe, Tsohon Gwamna Na Hannun Daman Wike Ya Faɗi Wanda Zai Goyi Baya a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Susan ta bayyana cewa matar tace duk wanda zai aikin za'a ɗaure masa ido lokacin da zasu sadu. Kuma zata rike shi har sai an tabbatar da ta samu juna biyu.

Babban dalilin da yasa za'a ɗaure wa mutumin ido shi ne don kar nan gaba ya dawo yana nemanta da ɗansa. Susan tace:

"Suzy dan Allah ki rubutu game da ni, ina bukatar mutumin da zai mun ciki, kyakkyawan mutum. Za'a ɗaure masa fuska duk lokacin da zai kwanta dani kuma zan biya shi."
"Abinda yasa za'a rufe masa fuska shi ne don kar ya dawo nan gaba yana nemana da ɗan, zan rikenshi har sai an tabbatar na samu ciki sannam zai tafi. Ina zaune a Abuja ni zan kula da komai na kuɗi."
"Dan Allah ki ɓoye sunana, tace kuɗin da zata biya miliyan uku cas."

Kara karanta wannan

Kyakkyawa Ce: Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Ji Da Tsawo Sanye da Takalma Masu Tsini a Ran Aurenta Ya Ja Hankali

Martanin mutane

Melodiesofpraise tace:

"Lallai kuwa, Allah yasa kar gobe ya dawo ya jefa ki cikin matsala, ya matsa miki sai kin nuna masa ɗansa, shawara ki bar matar ta nemi wanda zai mata aiki da kanta."

Queen Isaac Emejuru tace:

"Ki rufe idon ɗan wasu har sai kin ɗauki ciki, ya kenan idan ke ba mai ɗauka da wuri bace? Zaki ci gaba da rufe masa ido har tsawon shekara biyu kenan? Ya za'ai idan baki samu cikin ba, shin zaki biya ladan gwaji?"

Wata zankadediyar budurwa ta fashe da kuka kan rashin mashinshini

A wani labarin kuma Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan yaduwar bidiyon wata kyakyyawar budurwa da ta kasa auruwa.

Budurwar wacce ta bayyana cewa za ta cika shekaru 39 a bana tace har yanzu bata samu wani tsayayyen namiji ba.

Kara karanta wannan

Mutanen Jihata Zasu Angiza Wa Tinubu Tulin Kuri'unsu, Atiku Bai da Rabo, Gwamna Ya Magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel