Gwamna Zulum Ya Haramta Sayar da Barasa a jihar Borno, Ya Zargi Jami'an Tsaro

Gwamna Zulum Ya Haramta Sayar da Barasa a jihar Borno, Ya Zargi Jami'an Tsaro

  • Gwamna Babagana Zulum ya haramta siyar da giya a Borno, yana danganta hakan da karuwar laifuffuka da miyagun dabi’u a Maiduguri
  • Farfesa Zulum ya ce wasu sojoji da ‘yan sanda na cikin masu haddasa laifuffuka, yana mai cewa ba za a kyale kowa ba
  • Ya kafa kwamiti don rushe otal-otal da bariki marasa lasisi, tare da yaki da laifuka da ta da hankali a jihar baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya sanar da dakatar da siyar da barasa a fadin jihar.

Hakan ya biyo bayan zargin jami’an tsaro da Gwamna Zulum ya yi na haddasa laifuffuka a fadin jihar sanadin giya.

Gwamna Zulum ya hana siyar da barasa a Borno
Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya haramta siyar da barasa. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Original

Zulum ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake kaddamar da kwamitin rushe otal, bariki, da maboyar ’yan daba a gidan gwamnati, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Borno: Sojoji sun daƙile harin ƴan ta'adda

Hakan ya biyo bayan kokarin da jami'an tsaro ke yi na yakar yan ta'adda da kuma dakile aikata miyagun ayyuka a jihar.

Mayakan CJTF da ke aiki da rundunar Operation Hadin Kai sun dakile harin 'yan ta'adda a garin Izge da ke Gwoza a jihar Borno.

Dakarun sun kashe mayakan ISWAP guda uku tare da kwato bindigar harbo jirgin sama da babura uku da 'yan ta'addan ke amfani da su.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa babu asarar rayuka daga bangaren fararen hula yayin harin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.

Zulum ya hana siyar da barasa a Borno

Gwamna Zulum ya bayyana farin cikinsa ganin yadda jami'an tsaro ke wurin yana tambayar mafi yawan laifuffukan su wa ke aikata su?

A cewar Gwamna Zulum:

“Ina farin cikin ganin cewa jami’an soji da ’yan sanda na nan, domin mafi yawan laifuffukan nan, wa ke aikata su?

“Wasu tsofaffin sojoji, tsofaffin jami’an tsaro, da ma masu aiki yanzu ne ke aikata wasu, haka ma wasu fararen hula.
“Don haka, ba za a bar kowa ba, idan har muna so mu magance ta’addanci da miyagun laifuffuka a Maiduguri da jihar baki daya.”
Dalilin Zulum na haramta barasa a Borno
Gwamna Babagana Zulum ya hana siyar da barasa a Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Facebook

Musabbabin haramta siyar da barasa a Borno

Zulum ya zargi jami’an tsaro da zuga fararen hula aikata laifuffuka, karuwanci da sauran miyagun dabi’u da ke haddasa matsalar tsaro.

Ya ba kwamitin karfin guiwa don yakar miyagun mutane a Maiduguri da kewaye, da kuma dakile lalacewar tarbiyya a cikin al’umma.

Gwamnan ya ce haramta barasa na da nasaba da yawaitar kungiyoyin asiri, fada tsakanin bata gari, da kisan gilla a Borno, Channels TV ta ruwaito.

Zulum ya hada da sojoji, ’yan sanda, NSCDC da 'Civilian JTF' a cikin kwamitin domin tabbatar da cikakken yaki da laifuka.

Zulum ya yiwa ministan Tinubu martani

A baya, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taɓo batun kalaman da ministan yaɗa labarai ya yi kan matsalar tsaro a jihar.

Farfesa Zulum ya bayyana ministan cewa bai san abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan ba.

Zulum ya nuna cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin shawo kan matsalar ƴan ta'addan Boko Haram.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.