An Zo Wajen: Ministan Tinubu Ya Fadi Sharadin Karbar Kwankwaso a APC
- Ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ba su maraba da Rabiu Musa Kwankwaso a APC
- Ministan ya nuna cewa Kwankwaso bai da wani tasiri shiyasa yake so ya samu mafaka a jam'iyyar APC mai mulkin kasa
- Rt. Hon. Yusuf Ata ya nuna cewa jar hula ta Kwankwaso ta zama tarihi a Kano, domin a yanzu maganar APC kawai ake yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wasu shugabannin APC a jihar Kano, ciki har da ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Ata, sun yi magana kan yiwuwar komawar Rabiu Musa Kwankwaso jam'iyyar.
Jiga-jigan na APC sun nuna rashin amincewa da shirin sauya sheƙa da tsohon gwamnan na jihar Kano, ke yi daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Source: Facebook
Yusuf Ata ya yi magana da manema labarai ne bayan wani taro da suka yi da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan
APC ta nakasa shirin Atiku, ƴan takarar gwamna 2 da mambobi 12,000 sun bar PDP da ACP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene sharaɗin karɓar Kwankwaso a APC?
Ministan ya ce jar hula ta Rabiu Musa Kwankwaso tana shirin ɓacewa gaba ɗaya a jihar Kano.
Ya ce, sai dai idan shugaban APC na ƙasa, wanda shi ne jagoran jam’iyyar a jihar Kano, ya yanke shawarar karɓarsa, idan ba haka ba, Kwankwaso zai ci gaba da zama wanda ba su so a APC.
Yayin da yake nuna goyon baya ga jagorancin APC ƙarƙashin Ganduje a matakin jihar da na ƙasa, Ata ya godewa Shugaba Bola Tinubu tare da tabbatar masa da nasarar da za a samu a Kano a zaɓe mai zuwa.
Ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar na ƙasa yana aiki dare da rana don ganin an samu gagarumar nasara a Kano.
“Duk wanda ya kai ziyara jihar Kano ko a yau, zai ga canje-canje da dama. Da wuya ka ga jar hula a Kano. A da idan ka shiga masallaci sai ka ga jar hula da dama, amma a yau, idan mutane 5000 suka zo sallah, wataƙila ba ka ganin jajayen huluna fiye da 20."

Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta ƙara nakasa El Rufai da Kwankwaso, jiga jigai sun bar PDP da NNPP
“Don haka muna tabbatarwa shugaban ƙasa cewa ba ma buƙatar komai. Muna goyon bayan shugaban jam’iyyarmu na ƙasa. Muna tattaunawa da shi. Wannan ra’ayin ne na ɗaukacin ƴan APC na jihar Kano har a matakin ƙasa da ƙananan hukumomi."
"Kwankwaso ba ya da tasiri a Kano yanzu. Shi ne ke neman shiga APC, ba wai mu muka gayyace shi ba, domin siyasarsa na shirin mutuwa."
“Ba ya da tasiri. Don haka yana ta ƙoƙarin ganin an karɓe shi a APC. Hakan na iya janyo rikici a jam’iyyar APC a jihar Kano. Wannan shi ne matsayarmu.”
- Yusuf Abdullahi Ata

Source: Facebook
Minista bai son Kwankwaso ya shigo APC
Ministan ya bayyana cewa bai jin daɗin ganin Kwankwaso a cikin jam'iyyar APC. Da aka tambaye shi dalili, sai ya ka da baki ya ce:
"Ni a karan kaina ba zan ji daɗi ba, sai dai idan babanmu (Ganduje) ya yanke shawarar karɓarsa. Na kasance ɗan majalisar jiha a 1999 lokacin da Kwankwaso ke gwamna. Don haka na san Kwankwaso ƙwarai da gaske."
Baba-Ahmed ya ba Kwankwaso shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai ba Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya ba Rabiu Musa Kwankwaso shawara kan zaɓen 2027.
Hakeem Baba-Ahmed ya buƙaci tsohon gwamnan na jihar Kano da ya haƙura da yin takarar shugaban ƙasa a 2027.
Ya nuna cewa lokaci ya yi da tsofaffin ƴan siyasa irin su Kwankwaso za su koma gefe su ba sababbin jini waje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
