An Kama Jami'in Tsaro zai Sayar da Makamai ga 'Yan Bindiga a Arewa ta Yamma

An Kama Jami'in Tsaro zai Sayar da Makamai ga 'Yan Bindiga a Arewa ta Yamma

  • Hukumar DSS ta kama wani jami’in tsaro da ke sayar da makaman gwamnati ga ‘yan bindiga a jihar Kaduna, inda aka kama shi da tarin harsasai
  • An kama jami’in tare da wasu mutum 53 da suka haɗa da ‘yan bindiga, masu safarar makamai da iyalan wasu masu garkuwa a yayin samame a jihar
  • Gwamna Uba Sani ya yaba da nasarorin DSS karkashin sabon Darakta-Janar, Oluwatosin Ajayi, kan yadda suka ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wani jami’in tsaro da laifin sayar da makaman gwamnati ga ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’in, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, an kama shi da tarin makamai da ya shirya sayarwa 'yan ta'adda a kan Naira miliyan 4.

Uba Sani
An kama jami'in tsaro da zargin sayar wa 'yan bindiga makami. Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an cafke jami’in ne tare da wasu mutum 53 a jihar Kaduna yayin da DSS ke gudanar da samame a wuraren da ake zargin ana aikata laifuffuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama 'yan bindiga a jihar Kaduna

Baya ga jami’in tsaron, DSS ta kama wasu ‘yan bindiga takwas, masu bayar da bayanai ga 'yan ta'adda 22, masu safarar makamai huɗu da masu safarar mutane biyu.

The Guardian ta wallafa cewa an cafke masu zamba ta yanar gizo huɗu da masu lalata kayayyakin gwamnati biyu, tare da iyalan wasu da ake zargi da laifuffuka 12.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa an samu nasarar kama mutanen ne sakamakon kokarin DSS a sammame sama da 34 da suka kai a jihar.

Gwamna Uba Sani ya yaba wa shugaban DSS

Gwamna Uba ya bayyana gamsuwarsa da sabon Darakta-Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi, ya ce nada shi da aka yi ya taimaka wajen farfaɗo da hukumar.

Ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Shari’a na jihar Kaduna, Sule Shuaibu (SAN), bayan ziyararsa zuwa hedikwatar DSS a Kaduna.

Kwamishinan ya ce DSS ta kwato bindigogi da dama, bindigun Pump Action da dubban harsasai a zangon farko na shekarar 2025.

Uba Sani
Gwamnatin Kaduna ta yaba wa shugaban DSS kan kama masu laifi. Hoto: Uba Sani
Asali: UGC

DSS sun ceto mutane da dama a Kaduna

Daga cikin makaman da aka kwato akwai bindigogi AK-47 guda biyar, bindiga GPMG guda ɗaya, bindigun RPG guda uku da harsasai sama da 5,000.

Baya ga haka, jami’an DSS sun ceto mutum 79 da aka yi garkuwa da su, waɗanda yanzu suke hannun gwamnatin jihar domin kula da su.

An kama dan bindiga Dogo a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wani dan bindiga da ake kira Dogo a jihar Taraba.

Rahtanni sun nuna cewa Dogo na cikin manyan 'yan ta'addan da aka dade ana nema ido rufe a jihar saboda laifuffukan garkuwa.

Baya ga kama Dogo, sojoji sun kama wani mutum da ake zargi da cutar mutane ta hanyar damfara yana cewa shi soja ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng