"Sauƙi Ya Kara Samuwa": Farashin Fetur Ya Karye a Gidajen Man NNPCL a Najeriya
- Sauki na ta kara samuwa a Najeriya da kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya rage farashin litar man fetur a gidajen mai a Abuja da Legas
- Rahotanni sun bayyana cewa a yau Litinin, 21 ga watan Afrilu, 2025, NNPCL ya sauke farashin kowace lita zuwa N880 a Legas, N935 a Abuja
- Ana kyautata zaton wannan ragi da aka samu zai taka rawa wajen kawo sauƙi ga ƴan Najeriya musamman a wannan lokaci na tsadar rayuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya rage farashin litar man fetur (PMS) a wasu gidajen mai mallakinsa da ke cikin biranen Lagos da Abuja.
Wannan ragi na zuwa ne bayan matatar attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Ɗangote ra sauke farashin mai a ƙasar nan.

Asali: Original
Jaridar The Cable ta tattaro cewa a ranar Litinin, 21 ga watan Afrilu, 2025, NNPCL ya bi sahun matatar Ɗangote wajen rage farashin fetur a gidan man kamfanin na Abuja da Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya rage farashin fetur a Najeriya
An ruwaito cewa a wasu gidajen man NNPCL da ke jihar Lagos, ana sayar da lita kan N880, sabanin farashin da ke sayarwa a baya watau N925.
A babban birnin tarayya Abuja kuma, kamfanin ya rage farashin kowace lita daga N950 zuwa N935.
Binciken da aka gudanar a gidan man ya nuna cewa a gidan mai ka NNPCL da ke Apple Junction a jihar Legas, ana sayar da kowace lita kan N880.
Nawa ake sayar da fetur a gidan man NNPCL?
Haka nan kuma a gidan man Ago Palace da ke jihar Legas, NNPCL ya rage lita zuwa N905 yayin farashin gidan man kamfanin na titin Idimu da na titin Ikorun, kowace lita ta dawo N910.
A Abuja kuma rahoton ya tabbatar da cewa NNPCL ya rage farashin kowace litar fetur zuwa N935 a gidan mansa da ke kan titin filin jirgin sama a Lugbe.

Asali: Getty Images
Me ya kawo karyewar farashin man fetur?
Wannan ci gaba ya biyo bayan rage farashin man fetur da matatar Dangote ta yi a kwanakin nan, inda ta rage kowace lita zuwa N890.
A ranar 16 ga Afrilu, matatar Dangote ta ce wasu manyan abokan huldarta sun sauke farashin lita zuwa N890 a Legas daga tsohon farashi watau N920.
Rage farashin na iya saukaka wa 'yan Najeriya duba da wahalhalun tattalin arziki, koda yake har yanzu farashin ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da na shekarun baya.
Ana kuma sa ran hakan zai iya jawo sauran masu kasuwancin mai su bi sahun NNPCL da Ɗangote wajen sauke farashin.
Matatar Ɗangote ta rage farashi a gidaje 6
A wani labarin, kun ji cewa matatar Dangote ta jero gidajen man da 'yan Najeriya za su rika sayen mai a kan farashinta a sassan kasar nan.
Wannan na zuwa ne bayan matatar hamshaƙin attajirin ta ɗauki matakin rage farashin lita guda ta mai daga N865 zuwa N835 ga abokan huldarta.
Gidajen man MRS Oil, AP (Ardova), Heyden Petroleum, Optima Energy ns cikin gidajen da matatar ta ce ana samun mai a farashinta mai rahusa.
Asali: Legit.ng