Wata Sabuwa: Tinubu Ya Sauya wa Wasu Manyan Sakatarorin Tarayya 4 Wurin Aiki
- Shugaba Bola Tinubu ya sauya wa wasu manyan sakatarori hudu ma'aikatu domin karfafa aikin gwamnatin tarayya da yi wa al'umma hidima
- Wata sanarwa daga ofishin shugabar ma’aikata ta ce matakin ya yi daidai da manufar Renewed Hope Agenda na gwamnatin Bola Tinubu
- Za a kammala dukkanin sauye-sauye da mika aiki a ma'aikatun tarayyar kafin ranar 2 ga Mayu, 2025, kamar yadda shugaban kasa ya umarta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – A wani mataki mai ban mamaki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya wurin aikin wasu manyan sakatarorin tarayya hudu.
An bayyana wannan sauyi a matsayin wani bangare na kokarin da ake ci gaba da yi don karfafa ayyukan ma’aikatar gwamnatin tarayya da inganta ayyukan jama’a.

Asali: Twitter
An sauya wa manyan sakatarori 4 wuraren aiki
Bayani game da sauyin wurin aikin na cikin wata sanarwa da daraktar sadarwa, ofishin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mrs. Eno Olotu, ta fitar, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce sauya wa sakatarorin wuraren aiki ya yi daidai da manufar Renewed Hope Agenda na gwamnatin Tinubu, domin inganta dabaru da kwarewa a ma’aikatun gwamnati.
"Wannan sauyin guraben aiki na cikin ci gaba da kokarin kara inganta ayyuka, kirkiro sababbin hanyoyi da dabarun yi wa al'umma hidimina a ma’aikatar tarayya."
- Mrs. Eno Olotu.
Sakatarorin da Tinubu ya sauya wa wurin aiki
Ga jerin sunayen manyan sakatarorin da abin ya shafa da kuma sabbin wuraren aikinsu, kamar yadda Premium Times ta ruwaito:
1. Dr. Mary Ada Ogbe
An sauya mata wurin aiki daga ma’aikatar harkokin ma’adanai zuwa ma’aikatar ci gaban yankuna, inda za ta yi aiki tare da sakataren da zai yi ritaya a ranar 7 ga Mayu, 2025.
2. Injiniya Faruk Yusuf Yabo
An dage Injiniya Faruk daga ma’aikatar sadarwa, fasaha da tattalin arziki na zamani zuwa ma’aikatar harkokin ma’adanai.
3. Dr. Emeka Vitalis Obi
Shugaba Tinubu ya sauya wa Dr. Emeka wurin aiki daga ma’aikatar kasafin kudi da ci gaban tattalin arziki zuwa ma’aikatar albarkatun man fetur.
4. Mr. Ogbodo Chinasa Nnam
Shi kuwa Mr. Ogbodo, an sauya masa wurin aiki ne daga ofishin ayyuka na musamman (OHCSF) zuwa ma’aikatar sadarwa da wayar da kan jama'a ta kasa.

Asali: Twitter
An fadi lokacin kammala mika ragamar aiki
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mrs. Didi Esther Walson-Jack, ta bayyana cewa sauyin aikin wani mataki ne na al’ada domin kai kwararrun ma'aita inda ake da bukatarsu.
Ta bukaci sababbin sakatarorin da aka sauya masu wurin aiki da su yi amfani da kwarewarsu wajen ci gaban ma'aikatun da suka koma da kuma tabbatar da ingantaccen aiki.
Shugaban kasar ya ba da umarnin cewa a kammala dukkanin tsare-tsaren sauye-sauyen da mika aiki kafin ko zuwa 2 ga Mayu, 2025.
Tinubu ya nada manyan sakatarori 8
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin wasu sababbin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya guda takwai.
Nadin ya biyo bayan gibin da ritayar wasu sakatarori ya haifar, inda aka cike guraben da sababbin jami'ai masu cancanta daga sassa daban-daban.
An zabi sababbin sakatarorin daga jihohin Bauchi, Zamfara, da Jigawa dake Arewa maso yamma da kuma yankin arewa maso gabas na Najeriya.
Asali: Legit.ng