Murna Yayin da Shugaba Tinubu Ya Ƙara Yin Muhimman Naɗe-Naɗe Guda Biyu

Murna Yayin da Shugaba Tinubu Ya Ƙara Yin Muhimman Naɗe-Naɗe Guda Biyu

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa manyan sakatarori biyu a ma'aikatun gwamnatin tarayya
  • Tinubu, a wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, ya naɗa mutanen ne a ma'aikatar kudi da ma'aikatar albarkatun man fetur
  • Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan shugaban ƙasar ya rantsar da manyan sakatarori takwas a fadarsa da ke birnin Abuja ranar Litinin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da naɗin sabbin manyan sakatarori biyu a ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Shugaban ƙasar ya naɗa manyan sakatarorin ne a ma'aikatar kuɗi da ma'aikatan albarkarun man fetur ta ƙasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shugaba Tinubu ya sake naɗa shugaban kamfanin man fetur na ƙasa da wasu mutum 8

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabbin Manyan Sakatarori Biyu a Ma'aikatun Tarayya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Waɗan nan sabbin naɗe-naɗe biyu masu muhimmanci na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Okokon Ekanem Udo a matsayin babban sakataren ma'aikatar kuɗi ta tarayya.

Yayin da a ɗaya ɓangaren kuma Bola Tinubu ya naɗa Ambasada Gabriel Aduda a matsayin babban sakataren ma'aikatar albarkatun man fetur.

Sanarwan ta ce:

"Shugaban ƙasa Tinubu ya amince da naɗin manyan sakatarori biyu, Mista Okokon Ekanem Udo a matsayin babban sakataren ma'aikatar kuɗi da Gabriel Aduda a matsayin babban sakataren ma'aikatan albarkatun mai."

Wannan na zuwa ne awanni bayan shugaban ya rantsar da sabbin manyan sakatarori takwas da ya naɗa a baya-bayan nan.

Tinubu ya ba su rantsuwar kama aiki ne jim kaɗan gabanin fara taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) wanda ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Sakkwato

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama a Shari'ar Zaben Sokoto

A wani labarin na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato a zaben watan Maris, 2023.

Kwamitin alƙalan kotun ya ce hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yanke na korar karar PDP da ɗan takararta ya yi daidai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel