Sauya Sheka: Tsohon Gwamna, Bafarawa Ya Fallasa Abin da 'Yan Siyasa ke Nema a APC

Sauya Sheka: Tsohon Gwamna, Bafarawa Ya Fallasa Abin da 'Yan Siyasa ke Nema a APC

  • Tsohon gwamna, Attahiru Bafarawa ya ce siyasar hamayya ta mutu a Najeriya, saboda ’yan siyasa na sauya sheka ba don talaka ba
  • Ya kara da zargin ’yan siyasa da hamayya da junansu kawai, inda suke cika aljihunsu yayin da talaka ke fama da yunwa da jahilci
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa babu akida a siyasa, domin da zarar wata kofa ta rufe, ’yan siyasa na komawa inda suka fito ba kunya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Tsohon Gwamnan Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya caccaki ’yan siyasar kasar nan kan yadda suke sauya sheka ba tare da adawa ta hakika ba.

Ya zargi ’yan siyasa da cewa yanzu suna hamayya ne da junansu, musamman wajen neman mukamai da cika aljihunsu, ba don talaka ba.

Bafarawa
Bafarawa ya caccaki 'yan siyasa Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

A wata hira da BBC Hausa, Attahiru Bafarawa ya ƙara da cewa a halin da siyasar Najeriya ke ciki yanzu, babu wata sahihiyar hamayya ko fafutuka da ake yi saboda talaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene abin da ’yan siyasa ke nema a APC?

Alhaji Attahiru Bafarawa ya yi zargin cewa ’yan siyasar kasar na fafatawa da juna ne kawai domin samun mukamai, ba don wata akida ba.

Tsohon gwamnan ya ce:

“Saboda haka cikin duhu ake – da mai nema da wanda ake nema. Shi mai nema idon shi sun rufe: ba imani, ba tausayi – shi dai ya samu mukami.
"Shi kuma talaka idonshi sun rufe: ga yunwa, ga talauci, ga jahilci. Saboda haka duk a yamutse ake.”
Attahiru
Tsohon gwamnan Sakkawato, Attahiru Bafarawa Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Har ila yau, Alhaji Bafarawa ya ce:

“Adawar da ake yi, kowa kansa yake yi wa adawa. Idan ya ga waccan kofar ta rufe, bai jin kunya, bai jin tsoro. Hanyar da ya bata, zai bace, sai ya dawo ta nan.”

Bafarawa ya soki son zuciya da cin hanci

Tsohon jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa halin son zuciya na ’yan siyasa ne ya jefa Najeriya cikin halin da take ciki yanzu.

A kan batun rawar da talakawa ke takawa wajen sayar da kuri’arsu a ranar zabe, tsohon gwamnan ya ce ba laifin ’yan Najeriya ba ne kai tsaye.

Ya yi zargin cewa ’yan siyasa sun riga sun tsiyatar da jama’a, wanda ke sa wasu ba sa iya kai zuciyarsu nesa wajen karɓar kuɗi kaɗan don sayar da ’yancinsu.

Yadda Bafarawa ya fice daga PDP

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon Gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya sanar da ficewarsa daga babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa, wato PDP, bayan tsawon shekaru a cikinta.

Sanarwar ficewar tasa ta fito ne cikin wata wasiƙa da ya rubuta da hannunsa, wadda aka wallafa a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, 2025, amma bai sanar da jam'iyyar da zai koma ba.

Ficewar Bafarawa ta zo ne a daidai lokacin da PDP ke fama da rikice-rikice na cikin gida, musamman kan shugabanci da rashin jituwa tsakanin jiga-jigan jam’iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.