Namijin duniya: Ahmed Isa mutumin da yayi sanadiyyar gano yaran da aka sace a Kano

Namijin duniya: Ahmed Isa mutumin da yayi sanadiyyar gano yaran da aka sace a Kano

Kada mutane su manta da mutumin da yayi sanadiyyar gano yaran nan da aka sace a Kano. Mutumin dai sunan sa Ahmed Isah

Wannan bawan Allah shine sila ko sanadiyyar bankado satar yaran nan guda tara na Kano da rundunar 'yan sandan Kano ta yi nasarar kubutar da su daga Onitsha ta jihar Anambra.

Mutanen yankunan da lamarin ya shafa sun yi ta kai koken su wajen hukumomi da jami'an tsaro da gidajen rediyo na jihar Kano da kewaye, amma lamarin yana daukar lokaci ba tare da an dauki wani mataki ba.

Daga bisani dai mutanen sun yanke shawarar tuntubar Ahmed Isah a Abuja a gidan wani rediyo mai suna 'Human Right Radio 101.1 FM' a wani shiri mai suna 'Brekete Family'.

KU KARANTA: A gabana suka yiwa kanwata fyade sannan suka kashe mahaifina - Budurwa ta bayyana halin da suka shiga bayan 'yan bindiga sun kai musu hari har gida

A cikin wannan shiri ne mutanen da lamarin ya shafa suka bayyana koken su da cewa akwai wata mata da suke zargi da satar yaransu sama da hamsin wanda har kungiya suka kafa domin bin kadin wannan lamarin a wurare daban daban.

Bayan koken nasu Ahmed Isa ya kai korafin su inda ya kamata, cikin ikon Allah kuma gashi an samu har an binciko wadannan yara guda tara a cikin makon da ya gabata.

Muna yiwa wannan namijin duniya fatan Alkhairi. Allah yayi masa jagora, ya tsare dukkan 'yan uwa Musulmi fadawa irin wannan masifar. Amin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel