'Yan Sanda Sun Kama Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin 'Brekete Family'

'Yan Sanda Sun Kama Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin 'Brekete Family'

- Yan sanda sun kama Ahmad Isah mai gabatar da shirin Brekete Family

- Yan sandan sun gayyaci Ahmad Isah ne kuma ya amsa gayyatar amma ba a gan shi ba

- Daga bisani an sako shi sai dai ba a bayyana abin da ya faru tsakaninsa da yan sandan ba

Yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

'Yan Sanda Sun Kama Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin Brekete Family
'Yan Sanda Sun Kama Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin Brekete Family. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Bidiyon ya janyo muhawara a kafafen sada zumunta. Wasu da dama sun yi tir da abinda ya aikata yayin da wasu kuma suka goyi bayansa.

Tuni dai Isah ya nemi afuwa game da abin da ya aikata.

Da ya ke magana da Leadership a ranar Litinin, mai gabatar da shirin na Brekete Family ya ce yan sanda sun kama shi kan lamarin.

"Ina tare da yan sanda tunda safe a kan lamarin," ya shaidawa jaridar.

"Yan sanda sun kama ni saboda wannan lamarin."

Da ta ke tabbatar da kama shi a shafinsa na Twitter, kamfanin ta ce: "Ordinary President, Mai gabatar da Brekete Family kuma shugaban Brekete Radio ya amsa gayyatar da yan sanda suka yi masa zuwa ofishinsu da ke Kaduna a safen yau.

"Muna son jama'a su sani cewa mun kasa magana da shi kuma ba mu ganshi ba."

Amma, daga bisani an sako shi. Ba a bada bayani kan abin da ya faru a lokacin da ya ke tare da yan sandan ba.

A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel