Da Gaske an Biya Diyyar Naira Biliyan 6 ga Hausawan da aka Kashe a Edo?
- Gwamnatin Edo ta musanta zargin da IPOB ke yi cewa Gwamna Monday Okpebholo ya ware Naira biliyan 6 domin biyan diyya ga Hausawan da aka kashe
- Gwamnatin ta bayyana zargin a matsayin ƙarya da nufin haifar da rikici da raba kan al’umma, musamman bayan kisan fararen hula 16 'yan jihar Kano a Uromi
- An bayyana cewa babu wani kudi da aka amince da shi ko aka biya wasu mutane, tare da kira ga jami’an tsaro su binciki tushen ikirarin da IPOB ta yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Gwamnatin jihar Edo ta fito karara ta karyata zargin da ƙungiyar IPOB ke yadawa cewa an ware Naira biliyan 6 domin biyan diyya kan kisan Uromi.
'Yan ta'addan IPOB suna magana ne kan binciken da ake yi bayan kisan fararen hula 16 'yan jihar Kano da aka yi a jihar Edo.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa zargin ya fito ne daga wata sanarwa da IPOB ta fitar a ranar 21 ga Afrilu, inda ta yi ikirarin cewa gwamnatin Edo ta biya diyya mai tsoka ga 'yan Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma Gwamna Okpebholo ta bakin mai magana da yawunsa, Fred Itua, ya ce zargin karya ne, yana mai bayyana shi da cewa wani yunkuri ne na haddasa rikici da tayar da fitina a jihar.
Gwamnatin Edo ta biya diyyar Hausawa?
Itua ya bayyana cewa har yanzu ba a biya ko sisin kobo ga kowace ƙungiya ba, kuma babu wani kudurin da ya amince da biyan biliyan 6 da IPOB ke magana a kai.
A cewarsa, Gwamna Okpebholo ya je jihar Kano ne domin jajanta wa iyalan fararen hulan da lamarin ya shafa don hana daukar fansa daga Arewacin Najeriya.
Daga bisani, wata tawaga daga Kano ta ziyarci Edo domin tattaunawa kan diyya da samar da zaman lafiya mai dorewa, amma ba a cimma matsayar kudi ba.
An zargi IPOB da neman tayar da hankali
Sanarwar ta jaddada cewa IPOB na amfani da dabarar yada ƙarya da tayar da fitina a matsayin hanyar da ta saba bi, tare da ƙoƙarin shigo da rikicin ta cikin jihar Edo.
Gwamnatin ta ce jihar Edo ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na raba kan al’umma ba, kuma ta yi kira ga jami’an tsaro da su binciki waɗanda suka yada maganar.
Tribune ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Wannar ita ce dabi’ar IPOB ta yada ƙarya a karkashin abin da suke kira gwagwarmaya,”
“Yunƙurin jefa Gwamna Okpebholo cikin rikicin ƙungiyar IPOB ba zai yi nasara ba.”
Gwamnati ta jaddada cewa jihar Edo za ta ci gaba da zaman lafiya, haɗin kai da adalci ga kowa, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Asali: Twitter
An kama wani dan jihar Edo a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan dan KAROTA.
Lamarin ya faru ne a wajen gadar Muhammadu Buhari da ke jihar Kano a safiyar ranar Alhamis da ta wuce.
Matukin motar da aka kama dan asalin jihar Yobe ne, sai kuma wani mutum daya dan asalin jihar Edo da kuma wani dan jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng