N70,000: Albashin Jihohi Ya Karu da 90%, za a Kashewa Ma'aikata N3.87tn
- Kudin da aka ware domin albashi da alawus na ma’aikatan jihohi ya karu daga N2.036tn a 2024 zuwa N3.87tn a kasafin kudin 2025
- Rahoto ya nuna cewa jihohi 27 ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba tare da dogaro da kudin da ake rabawa daga gwamnatin tarayya ba
- Karin albashin N70,000 da karin mukamain gwamnati ne suka haddasa hauhawar kudin albashi a jihohin Najeriya a shekarar 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A kasafin kudin 2025 da aka amince da shi, an bayyana cewa jimillar kudin da jihohi 36 suka ware domin biyan albashi da alawus ya karu da kaso 90%, inda ya kai N3.87tn.
Duk da cewa jihohin sun ware N2.8tn domin albashi a bara, sun kasa biyan cikakken adadin, inda suka kashe N2.036tn kacal, wanda ya rage N764bn daga abin da aka tsara a kasafin kudinsu.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa karin na da nasaba da aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 da kuma karin mukaman siyasa, kamar yadda alkaluman kasafin kudin jihohi suka nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kara albashin ma'aikata a Najeriya
A watan Yuli 2024, Shugaba Bola Tinubu ya amince da karin mafi karancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 bayan tattaunawa mai tsawo da kungiyoyin kwadago.
Sai dai a lokacin wasu jihohi ba su fara aiwatar da sabon tsarin ba, lamarin da ya sa kungiyar NLC ta bai wa jihohi wa’adin fara aiwatar da sabon tsarin kafin 1 ga Disamba 2024.
Kudin albashi ya karu a jihohi a 2024
Rahoto ya nuna cewa jihohi 20 sun yi karin kudin albashi da ya haura kaso 50%, yayin da sauran jihohi 16 suka yi karin kasa da hakan.
Jihohin da suka fi samun karin fiye da kaso 100% sun hada da Abia, Cross River, Ekiti, Niger, Rivers, da Taraba.
A daya bangaren kuma, Gombe, Osun, da Ondo da suka jinkirta aiwatar da sabon tsarin albashi, karin da suka yi bai wuce kaso 15% ba.
Misali, jihar Abia ta kara kasafin kudin albashi daga N33.045bn zuwa N77.34bn, wanda ke nuni da karin kaso 134%.
Jihar Cross River ta samu karin kashi 202%, inda ta kara kudin albashi daga N35.02bn zuwa N106.12bn.
Karin albashi a jihohin Kano da Rivers
A daya bangaren, Kano ta kara albashin ma’aikata daga N89.97bn zuwa N150.996bn, wanda ya haura kaso 67.8%.
Haka kuma, jihar Rivers ta yi karin kaso 105.6%, inda kasafin kudin albashi ya tashi daga N167.05bn zuwa N343.196bn.
Matsalar dogaro da kudin gwamnatin tarayya
Rahotanni sun nuna cewa, daga cikin jihohi 36, jihohi 27 ba za su iya biyan albashi ba tare da dogaro da kudin da ake rabawa daga Abuja.
Jihohin da ke da karfin biyan albashinsu daga kudin da suke samarwa da kansu sun hada da Legas, Abia, Benue, Enugu, Ogun, Niger, Kaduna, Kwara da Osun.

Kara karanta wannan
An gabatar da bukatar kirkirar sababbin jihohi 31 a Najeriya, an jero su daga yankuna 6
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa hauhawar albashi yana da illa ga tattalin arzikin jihohi, musamman ma waɗanda ba su da wadatattun hanyoyin samun kudin shiga.
A cewar Darakta na Cibiyar Inganta Kasuwanci, Muda Yusuf (CPPE):
“Wasu jihohi na fama da ƙarancin kudin shiga saboda bambance-bambancen albarkatun da suke da su.
"Dole ne gwamnati ta rage yawan ma’aikatan da ba su da amfani, domin wasu ma ba sa zuwa aiki.”
Farfesa Segun Ajibola na Jami’ar Babcock ya ce jihohi su kara yawan kudin da suke samarwa da kansu ba tare da sanya wa talakawa haraji mai nauyi ba.
Haka zalika Farfesa Segun Ajibola ya bukaci jihohi su rage yawan kashe kudi, su hana almundahana a gwamnati.
Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar malaman firamare a jihar Ebonyi ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani kan albashi.
Kungiyar malamai ta NUT a jihar ta bayyana cewa sun tsunduma yajin aikin ne saboda rashin biyan su albashin watanni uku a wasu kananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng