'Kun Raina Shari'a': Kotu Ta Tsige Fitaccen Sarki daga Sarauta, Ta Gargadi Gwamnatin Jiha
- Kotu a jihar Ogun ta soke nadin Oba Olugbenga Shomade a matsayin Akufon na Idarika, tana cewa nadin ya saba doka kuma gwamnati ta raina kotu
- Mai shari’a Oloyede ya ce an nada Somade ne duk da umarnin hana haka, inda gwamnati ta ci gaba da nadin sarautarsa tun ranar 24 ga Yuli, 2024.
- Wata kara da aka shigar tun 23 ga Mayu, 2024, ta nemi kotu ta soke nadin, amma duk da haka aka ci gaba da nadin sarautarsa
- Kotu ta yanke hukunci cewa nadin da sarautar Shomade ba su halatta ba, ta kuma soke takardun shaidar nadin da aka ba shi a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Wata babbar kotu a jihar Ogun ta soke nadin Oba Olugbenga Shomade a matsayin Akufon na Idarika, Iperu Remo, a karamar hukumar Ikenne.
Kotun ta ce nadin da gwamnatin jihar ta yi ya sabawa doka inda ta gargadi gwamnatin jihar Ogun kan shiga lamarin sarautar.

Asali: Original
Kotu ta kalubalanci gwmana kan nadin sarauta
A hukuncin da aka yanke a ranar 5 ga Maris, Mai shari’a O. S. Oloyede ya bayyana nadin Shomade a matsayin raini ga doka, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne kasa da makwanni biyu bayan babbar kotun jihar Ogun ta dakile matakin da gwamna Dapo Abiodun ya dauka kan lamarin sarauta.
Babbar kotun mai zama a Abeokuta ta soke naɗin sarkin Olawo, Alexander Macgregor har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin ƙarshe.
Mai shari'a Olatokunbo Majekodunmi ta ce naɗa basaraken da gwamnan Ogun ya yi, ya saɓawa tanadin doka kuma ya raina kotu.
Daga bisani, kotun ta kuma ba da umarnin a kwace sandar mulki da sauran takardun naɗin da gwamnati ta ba Macgregor, ta ce sai an jira hukuncin da za ta yanke.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

Asali: Facebook
Kotu ta tsige Sarki daga sarauta a Ogun
Alkalin kotun ya ce gwamnatin Ogun ba ta da hakkin kaddamar da basaraken bayan an shigar da kara.
Kotun ta bayyana cewa Pa Fasasi Ogunmuyiwa da Moshood Onakoya, madugunan gidan sarauta na Igun, sun shigar da kara tun 23 ga Mayu, 2024, suna neman kotu ta soke nadin.
Mai shari’a ya ce gwamnati ta ci gaba da nadin Shomade duk da an aika musu da bukatar hana hakan wanda ya fusata kotu da kuma raini gare ta.
Saboda haka, kotun ta tabbatar da soke nadin da kuma takardun nadin sarauta da aka ba shi, Daily Post ta ruwaito.
Basarake ya dakatar da hakimai 67 a Edo
A baya, mun ba ku labarin cewa Mai Martaba Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya dakatar da hakimai 67 daga sarautarsu saboda rashin biyayya ga fada.
Majalisar gargajiya ta Benin ta bayyana cewa hakiman sun aikata abubuwan da ke nuni da cin fuskar sarki da masarautar.

Kara karanta wannan
Magana ta ƙare, Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan ƴan Majalisa 27 da suka 'koma' APC
Sai dai da dama daga cikin wadanda aka dakatar sun kai karar sarkin a kotu, suna cewa ba shi da ikon dakatar da su daga yin hakimci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng