Jerin makamai 9 da hukumar 'yan sanda ta haramta amfani da su
A kokarin ta na yaki da aikata miyagun laifuka, hukumar 'yan sandan Najeriya ta fitar da jerin wasu makamai da sinadarai guda 9 da samun su a hannun farar hula laifi ne da kan iya jawo wa mutum gurfana gaban shari'a.
A ranar 21 ga wata ne shugaban hukumar 'yan sandan Najeriya, Ibrahim K. Idris, ya aike da wani umarni ga kwamishinonin hukumar dake jihohin Najeriya da mataimakan sa na musamman dake shiyyoyi 12 na kasar nan da su fara aikin kwato makamai daga hannun 'yan kungiyar ta'adda da tayar da kayar baya da ma farar hula da a kan iya amfani da su domin tayar da fitina.
Rukunin makaman sun hada da:
1. Majaujawa
2. Kayan sinadarin gas da kan iya fashewa
3. Bam da gurneti
4. Makamin Roket
5. Bindigu: Manya da kanana
6. Bindigun soji
7. Bindigu masu zobe
8. Bindigar Baushe
9. Duk wani makami da za a iya kisa da shi
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an kafa kwamitin da zai tilasta jama'a biyayya da wannan umarni.
KARANTA WANNAN: Wani mutum ya daddatsa wani matshi da adda a Abuja
Kazalika hukumar na kira da duk wata kungiya da ba mallakar gwamnati ba, irin su bijilante, da su guji daukar makamai masu hatsari.
Kazalika hukumar ta ce ba zata bayar da lasisi ga kowa ba domin mallakar irin wadannan makamai.
Hukumar 'yan sanda Najeriya ta bukaci jama'a da su gaggauta sanar da ita duk wani mutum da suka gani dauke da irin wadannan makamai a kan lambobin waya kamar haka: 08037025670, 08032451594, 08036783383, 09098049333.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng