An Gano Wani Wuri da Aka Ce Yana Ɗauke da Sawun Kafar Annabi Muhammad SAW a Kano
- Hukumar Hisbah ta lalata wani wuri da mutane suka fara raɗe-raɗin yana ɗauke da sawun kafar Annabi Muhammad (SAW) a Kano
- Rahotanni sun nuna cewa tuni, mata da yara suka fara baibaye wurin, wamda aka ce ruwa na ɓulɓulowa domin neman tabarraki
- Hisbah ta ja hankalin mutanen jihar Kano da cewa wannan sani salo ne na yaudara saboda ba shi da tushe a addinin musulunci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta lalata wani wurin da mutane suka fara kallonsa a matsayin wurin ibada, biyo bayan rade-radin cewa wurin na dauke da sawun kafar Annabi Muhammad (SAW).
Rahotanni sun nuna cewa tun kwanakin baya hukumomi suka share wurin, wanda ke yankin masana'antu na Dakata domin aikin layin dogo.

Asali: Twitter
Yadda aka fara raɗe-raɗin an ga sawun Annabi
Leadership ta tattaro cewa a yanzu wurin ya fara janyo hankalin jama'a bayan an ga wani sawun kafa a cikin laka, sannan kuma ruwa na ɓulɓulowa daga wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya sa dubban mutane suka fara tururuwa zuwa wurin domin shan ruwa, wanka, da ɗaukar ruwan a cikin robobi suna zaton yana da wata daraja kuma ya na magani.
Bidiyoyi a kafafen sada zumunta sun nuna yadda mata da maza da yara ke cakusawa wajen samun damar ɗibar ruwa daga wurin,
Wasu ma har sujada suke yi da yin addu’o’i, wasu kuma na yin wanka ko ɗaura alwala da ruwan.
Hukumar Hisbah ta ɗauki mataki
Da yake martani game da lamarin, Mataimakin Kwamandan Hisbah na Kano, Muhahideen Aminudeen, ya ce hukumar ta samu rahotanni game da abin da ke faruwa kuma ta hanzarta tura jami’anta domin dakile lamarin.
Ya bayyana ikirarin da aka yi a matsayin ƙarya mai hadari, musamman duba da rashin wani tushe na tarihi ko addini da ke tabbatar da cewa sawun kafar Annabi ne.
“Wasu mutane ne mayaudara suka ƙirkiri wannan labari mara tushe cewa wurin ya zama mai tsarki wai saboda Annabi SAW ya taka.
"Abin takaici, mutane da dama da basu da cikakken ilimin addini sun fada tarkon wannan karya,” in ji shi.

Asali: Facebook
Annabi SAW ya taɓa zuwa Kano a tarihi?
Muhahideen Aminudeen ya kara da cewa Annabi Muhammad (SAW) bai taba zuwa Afrika ba, balle kuma jihar Kano.
Ya ja hankalin jama’a da su nemi ilimi mai inganci na addinin Musulunci domin kauce wa irin wadannan rudani.
“Irin wannan jita-jita na iya jefa mutane cikin halaka, kuma har yana iya zama barazana ga lafiyar jama’a,” in ji shi.
Ya kuma gargadi jama’a da kada su ci gaba da shan ruwan wurin, domin mai yiwuwa ya na dauke da guba saboda kasancewar yankin yana kusa da wuraren masana'antu.
Malam Sadiq Madabo ya wallafa bidiyon a shafin Facebook, ya na mai takaicin yadda wasu Bayin Allah suka biyewa zancen.
Matashin malamin ya yi tir da yadda maza da mata su ke cakudawa da sunnan tabarruki.
"Haka wasu ke kwana su wuni gurin nan, wai an ce: Sahun ƙafafu Annabi ﷺ ya bayyana a gurin. Hisbah sun kore su, sun sake taruwa.
Wasu na zuba ruwa su sha, wasu na kwanciya su yi burgima, duk da sunan neman tabarruki.
Ko a tarihi, Annabi ﷺ bai taɓa zuwa Afrika ba ma, amma an ci galaba akan tunaninsu cewa yau a Hotoron Arewa, sahun ƙafafunsa masu tsarki da albarka sun bayyana😢
Kuma tsakaninsu da Allah, yaƙininsu kenan..🥲
Wallahi har cikin ransu su na son Annabi ﷺ ne, sai wasu ke amfani da wannan su ɗora su kan ɓata, yaudara da saɓawa koyarwarsa ﷺ
Babban ɓacin rai, ikhtilaɗin maza da mata. Can wasu ba muharramansu ba, na gogayya da su. Inna lillAhi wa inna iLaihi raji'un!😢
Yaa Rabb! Ka haskaka zuƙatan da duhun jahilci ya lulluɓe da ilmi da hidaya.!
- Sadiq Madabo
Daurawa ya yi martani ga Ɗan Bello
A wani labarin, kun ji cewa babban kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana kan zargin shugaban Izala na ƙasa da almundahana.
Malam Daurawa ya ce Allah ya ba Sheikh Abdullahi Bala Lau arzikin da ya fi karfin da ci kuɗin da ba na shi ba.
Daurawa ya nuna damuwa kan yadda fitaccen mai fadakarwa nan da tone-tonen almundahana, Dan Bello ya jefi shugaban Izala da badakalar kwangiloli
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng