Dan Bello: Sheikh Daurawa Ya Yi Martani a kan Zargin Shugaban Izala da Almundahana

Dan Bello: Sheikh Daurawa Ya Yi Martani a kan Zargin Shugaban Izala da Almundahana

  • Shugaban Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce Abdullahi Bala Lau na da isasshen arziki da zai hana shi yin almundahana
  • Daurawa ya nuna damuwa kan yadda fitaccen mai fadakarwa da barkawanci, Dan Bello ya jefi shugaban Izala da badakalar kwangiloli
  • Sai dai Shehin ya bayyana yakinin cewa wadannan maganganu da zarge-zarge sun zo karshe saboda an fara bata magada Annabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce shugaban Izala na Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yana da arzikin da zai kore masa yin almundahana

Ya bayyana haka ne a taron da’awa da ya gudana a Turai, inda ya yi martani ga Bello Galadanchi, wanda aka fi sani da Dan Bello bayan ya zargi Sheikh Bala da almundahanar wata kwangila.

Izala
Daurawa ya yi martani ga kalaman Dan Bello a kan shugaban Izala Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa/Dan Bello
Asali: Facebook

A bidiyon da DCL ta wallafa a Sheikh Daurawa ya zargi Dan Bello da kokarin bata suna da taba mutuncin malamai a fadin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Daurawa ya ce a kan Dan Bello

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya zargi Dan Bello da dauko maganar yayata labarin da ba shi da tushe, domin bata sunan malamai.

Ya ce:

“Da yana ta zagin ‘yan siyasa, ya ce ya binciko kaza, ya binciko kaza, sai kuma ake ga ai lokaci ya yi da za a fara taba mutuncin malamai.
Sai ya zo ya fadi maganganu marasa hujja, marasa dalili, marasa karko, marasa kyau ga Shugaba Sheikh Bala Lau.”
“Tun da na ji wannan, na ce to, wannan abin karshensa ya zo. Malaman nan fa ba ma’asumai ba ne, malaman nan fa ba mala’iku ba ne, masu karantar da sunnah ne, masu karantarwa ne, masu koyarwa ne, masu son a yi alkhairi ne.

Kai, ko kuskure malami ya yi, ya kamata ka roka masa gafarar Allah, ka nema masa afuwa."

Daurawa ya magantu kan zargin karbar kwangila

Shugaban hukumar Hisbah ya bayyana cewa yanzu haka mata masu yawon banza ne ke karbar kwangilar biliyoyi daga jami’an gwamnati a kasar nan.

Izala
Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala lau Hoto: Abdullahi Bala Lau
Asali: Facebook

Sheikh Daurawa ya ce:

“Ko da a ce Sheikh Bala Lau ya na da asusu 200, bai karya dokar Najeriya ba. Akwai karuwa da aka ba ta kwangila ta biliyan daya. Akwai abin da nake nema a wani ofis, wani ya ce min, ‘Malam, kar ka sha wahala, zan hada ka da karuwar mai wannan ofis din, za ta yi masa magana, za a kawo abin.’”

Ya bayyana takaicin yadda karuwai da ‘yan daudu ke cin moriyar kwangilar gwamnatin kasar nan fiye da malamai da sauran mutanen kirki.

Izala za ta maka Dan Bello a kotu

A baya, kun samu labarin cewa Kungiyar Izala ta bayyana aniyarta ta maka Dan Bello a kotu, bisa zargin ɓata suna da ya yi wa shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta musanta zargin da Dan Bello ya yi cewa kungiyar ta karɓi kuɗi daga gwamnati don gina ajujuwa amma ba a yi aikin ba.

Daga cikin ayyukan da ake magana a kai akwai wanda Hon. Mukhtar Aliyu Betara, dan majalisar wakilai mai wakiltar Bayo/Biu/Kwaya-Kusar, ya dauki nauyi a wani yanki da ke da alaka da Izala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.