Jami'an Hukumar Hisbah Sun Ƙwace Kwalaben Giya 8,400 a Kano
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi nasarar kama wata mota dauke da giya a Kano
- Jami'an na Hisbah da suka kama direban motar sun ce ya fito ne daga Zaria zai shiga Kano
- Hukumar ta sake jaddada cewa haramun ne sayar da giya ko kayan barasa a Kano domin suna gusar da hankali
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kwace kwalaben giya guda 8,400 a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Kura a jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Babban kwamandan hukumar ta Hisbah, Dakta Harun Ibn-Sina, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Talata a Kano.
DUBA WANNAN: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi
A cewar sanarwar, "Motar ta fito daga Zaria ne tana hanyar zuwa Kano a lokacin da jami'an na hukumar Hisbah suka kama direban.
"Hukumar ta Hisbah ta hana sayar da giya a jihar da sauran kayayakin barasa don gudun gusar da hankali," in ji shi.
KU KARANTA: 2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa
Babban kwamandan na Hisbah ya kara da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin shari'a ta yanke hukunci.
A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.
Asali: Legit.ng