Kamfanin NNPCL Ya Kuma Rage Farashin Mai a Karon Farko bayan Sauƙe Mele Kyari

Kamfanin NNPCL Ya Kuma Rage Farashin Mai a Karon Farko bayan Sauƙe Mele Kyari

  • Kamfanin NNPC ya rage farashin litar man fetur zuwa N935 a wasu gidajen mai na Abuja, lamarin da ya faranta wa direbobi rai
  • Abdullahi Hashim daga Kubwa ya ce ya lura da sabon farashin tun safiyar Asabar, yana mai cewa hakan na da matukar amfani ga jama’a
  • Bukola Adewole ta tabbatar da ganin sabon farashin tun ranar Juma’a a Wuse Zone 4, kuma tashar mai ta Kubwa Expressway ta fara siyarwa shi
  • Wannan saukin farashi ya biyo bayan rahoton da matatar Dangote ta fitar, inda ta rage farashin man sa daga N865 zuwa N835 kowace lita

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kamfanin NNPC ya rage farashin litar man fetur a wasu gidajen mai a birnin Tarayya, Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sabon farashin yanzu ya kasance N935 a wasu gidajen mai da ke Abuja.

NNPCL ya rage farashin mai a Abuja
An yaba da kamfanin NNPCL ya rage farashin man fetur a Abuja. Hoto: NNPC Limited.
Asali: Facebook

Ƴan Najeriya sun ji dadin rage farashin mai

Wasu direbobi a Abuja sun tabbatar da wannan sabon farashi ga wakilin Punch da aka gani a wasu gidajen man da ke karkashin ikon NNPCL a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Hashim, mazaunin Kubwa, ya ce:

“Na lura da saukar farashin zuwa N935 kowace lita da safiyar Asabar. Wannan ci gaba ne mai kyau.”

Ita ma Bukola Adewole ta ce:

“Na fara ganin sabon farashin a Wuse Zone 4 ranar Juma’a. Gidan mai ta Kubwa Expressway yanzu ta fara nuna hakan.”
Wasu sun yabawa NNPCL kan rage farashin mai a Abuja
Kamfanin NNPCL ya rage farashin man fetur a wasu gidajensa da ke Abuja. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda Dangote ya rage farashin mai a baya

Wannan ci gaba ya biyo bayan sanarwar matatar man Dangote da ta rage farashin man sa daga N865 zuwa N835 kowace lita.

Masana’antar mai da ke fitar da gangar danyen mai 650,000 a rana ta bayyana cewa tashoshin MRS da AP za su sayar tsakanin N890 da N920.

Wasu rahotanni suka ce gidajen mai na MRS a Abuja ba su sayar da mai ba tun ranar Laraba, 16 ga Afrilu, bayan Dangote ya sanar da saukar farashi.

Legit Hausa ta zanta da wani a Abuja

Mahmud Muhammad wanda direba ne da ke jigila zuwa Abuja ya ce akwai gidajen mai da suke sayar da litar a N935.

"Ni dai ban siya ba amma abokin aiki na ya siya litoci da yawa a kan wannan farashi a wasu tsirarun gidajen mai."

- Cewar direban motar

Mahmud ya ce tabbas hakan yana sanya su cikin farin ciki duba da samun sauki a kudin mota.

Ya ce su kansu suna ganin akwai tsauwalawa al'umma masu tafiye-tafiye duba da halin da mutane ke ciki a yanzu.

An bukaci binciken Mele Kyari kan badakala

Kun ji cewa wata kungiya ta kwararru da 'yan ƙasa masu kishin Najeriya ta bukaci a binciki tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari, kan kashe $1.5bn.

Kungiyar ta yabawa Bola Tinubu bisa sauke Kyari, tare da cewa an zuba makudan kudi a gyaran matatar mai ba tare da haifar da 'da mai ido ba.

Ta ce akwai buƙatar kwakkwaran bincike kan bacewar ganga miliyan 89 na danyen mai da kuma yarjejeniyar mai da kamfanin Matrix.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.