Sauki Ya Kara Samuwa: Dangote Ya Sake Rage Kudin Fetur da 3.5% a Najeriya

Sauki Ya Kara Samuwa: Dangote Ya Sake Rage Kudin Fetur da 3.5% a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa matatar Dangote ta kara rage farashin litar man fetur daga N865 zuwa N835, an samu saukin kashi 3.5%
  • Sabon farashin litar ya biyo bayan faduwar farashin gangar danyen mai a kasuwar duniya daga $70 zuwa $64 a makon nan
  • Sauyin farashi yana kara matsa wa masu shigo da fetur daga ketare fuskantar barazanar asarar fiye da Naira biliyan 76 a kowane wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matatar Dangote ta sanar da rage farashin litar fetur zuwa N835 daga N865, wanda ya nuna cewa an samu ragin kashi 3.5% a cikin tsohon farashinsa.

Sauyin farashin ya biyo bayan faduwar farashin gangar danyen mai a duniya, wanda ya sauka zuwa $64 daga fiye da $70 a 'yan makonnin baya.

Kara karanta wannan

'Hanya 1 ce': Atiku Ya Saɓa da Gwamnonin PDP kan Haɗaka da Tuge Tinubu a Mulki

Dangote
Dangote ya sake rage kudin mai. Hoto: Dangote Industries|Getty Image
Asali: UGC

Rahotan Vanguard ya nuna cewa karyewar farashin danyen mai yana shafar kasuwannin mai na cikin gida Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta wallafa cewa rage kudin da Dangote ya yi ya zo ne kasa da makonni bayan kamfanin ya rage farashin daga N880 zuwa N865.

Sai dai duk da rage kudin da Dangote ya yi, ‘yan kasuwa ba su saukar da farashin ga masu saye kai tsaye ba a mafi yawan gidajen mai.

'Yan kasuwa na asarar shigo da mai

Tuni masana'antun man fetur da masu shigo da kaya suka fara fuskantar matsin lamba, kasancewar matatar Dangote na ci gaba da sauya yanayin kasuwar man fetur.

Masu shigo da man fetur sun bayyana asarar da suke yi a sakamakon raguwar farashin da Dangote ke yi ba zato ba tsammani, inda aka kiyasta asarar ta kai Naira biliyan 2.5 a kullum.

Matakin ragin farashin da Dangote ke yi na jawo hankalin masu sayen mai zuwa ga man da ya fi araha, lamarin da ke barazana ga masu shigo da man daga waje da ke fafutukar sayar da kayansu.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta ɓarke a PDP, gwamnoni 5 sun fara tunanin ficewa daga jam'iyya

Alakar saukin mai da ciniki da Naira

Duk da matsin lamba daga kungiyoyin kamar DAPPMAN, gwamnatin tarayya ta sake dawo da yarjejeniyar cinikayyar danyen mai da Naira, wadda ta dakatar da ita na dan lokaci a baya.

Bayan dakatar da tsarin ne farashin litar fetur ya tashi daga ₦860 zuwa ₦930, wanda ya janyo dawowar tsarin don tallafa wa masana’antun tace mai a cikin gida.

Masana sun ce wannan matakin yana nuna yunkurin gwamnati na rage dogaro da shigo da mai da kuma karfafa gwiwar masana’antu masu zuba jari a fannin tace mai a Najeriya.

Baya ga haka, ana ganin matakin na cikin abin da ya sanya matatar Dangote kara rage kudin litar man fetur a Najeriya.

Dangote
'Yan kasuwa na asara bayan Dangote ya rage kudin mai. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Alakar danyen mai da farashin kayan abinci

A wani rahoton, kun ji cewa masana sun bayyana cewa karyewar farashin danyen mai zai iya shafar farashin kayayyaki a Najeriya.

Legit ta rahoto cewa a yayin da ake samun saukar farashin danyen mai a kasuwar duniya, ana hasashen kudin sufuri zai sauka a Najeriya.

'Yan kasuwar man sun bayyana yawan hako mai da ake yi kwanan nan da kuma matakan da shugaban Amurka ke dauka a matsayin dalilan saukar farashin danyen mai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng