Rikicin Tinubu da Gwamnan Bauchi: Minista Ya Fadi Dalilin Rashin Jituwa

Rikicin Tinubu da Gwamnan Bauchi: Minista Ya Fadi Dalilin Rashin Jituwa

  • Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya zargi gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, da amfani da suka ga shugaban kasa Bola Tinubu domin fara kamfen din 2027
  • Yusuf Tuggar ya bayyana cewa sukar Bala Mohammed ba ta da cikakkiyar manufa, kuma ya yi amfani da batun kudirin haraji domin ya cimma burinsa na siyasa
  • Ministan ya yi martani ne kan kalaman gwamnan Bauchi na cewa kudirin harajin shugaba Bola Tinubu na iya kawo cikas ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yi zargin cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, yana sukar Tinubu domin manufa ta siyasa.

Yusuf Tuggar ya ce gwamnan na amfani da suka da ya yi wa shugaban kasa Bola Tinubu dangane da batun gyaran haraji domin ya fara kamfen din sa na shugabancin kasa a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

Bola Tinubu
Ministan ya fadi dalilin sukar gwamnan Bauchi ga Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Lawal Muazu Bauchi
Asali: Facebook

Tuggar ya yi wannan zargi ne a wata hira da aka yi da shi a wani shiri na gidan talabijin din Channels a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, gwamnan Bauchi ya yi amfani da wannan batun ba tare da wata manufa mai ma'ana ba, inda ya fi sauran gwamnoni zafafa maganganunsa a kan shugaban kasa da gwamnatinsa.

Martanin Tuggar ga gwamnan Bauchi

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya bayyana cewa wasu gwamnoni sun bi salo mai kyau wajen sukar kudirin haraji sabanin hanyar da gwamnan Bauchi ya bi.

Yusuf Tuggar ya bayyana cewa;

“Gwamna Bala Mohammed ya nuna cewa ba shi da cikakkiyar manufa da gaskiya a sukar da ya yi wa shugaban kasa Tinubu.
A gaskiya, wasu gwamnoni sun yi tambayoyi masu mahimmanci game da kudirin gyaran haraji lokacin da aka gabatar da shi,
Amma Bala Mohammed ya yi amfani da wannan damar domin ya fara kamfen din shugabancin kasa.”

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Maganar gwamnan Bauchi kan hudirin haraji

Yayin wani taro da al’ummar Kirista a lokacin bikin Kirsimeti a Bauchi, Bala Mohammed ya gargadi shugaban kasa Tinubu da ya dakatar da kudirin haraji saboda yana iya haifar da rikici.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan tsari ba zai taimaka wa yankin Arewa ba, yana mai cewa za a samu matsaloli wajen biyan albashi idan aka ci gaba da aiwatar da shi.

Gwamna Bala Mohammed ya ce;

“Idan aka ci gaba da irin wannan manufofi, za mu nunawa shugaban kasa asalin halinmu.”

Wannan maganar ta ja hankalin fadar shugaban kasa, wadda ta yi watsi da ita, tana mai bayyana zancen a matsayin barazana ga Bola Tinubu.

Gwamnan Bauchi ya nemi ganin Tinubu

Yusuf Tuggar ya kara da cewa gwamnan Bauchi ya yi kokarin ganin ya samu damar ganawa da shugaban kasa duk da sukar da ya yi wa kudirin gyaran haraji.

Kara karanta wannan

"Ban ƙwallafa rai ba": Peter Obi ya canja shawara kan kudurin zama shugaba ƙasa

Sai dai a bisa dukkan alamu gwamna Bala Mohammed bai samu ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba a lokacin.

Kwankwaaso ya yi raddi ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi martani ga gwamnatin tarayya kan tsaron Kano.

Sanata Kwankwaso ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta bari ana kirkirar barazanar tsaro ta karya ba domin cimma wata manufa ta daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng