Hausawan Legas Sun Watsar da NNPP, Sun Koma Tafiyar Barau Jibrin a APC

Hausawan Legas Sun Watsar da NNPP, Sun Koma Tafiyar Barau Jibrin a APC

  • Shugabannin al’ummar Arewa a Legas sun ziyarci mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin a Abuja
  • Wani dan Kwankwasiyya, Alhaji Abdullahi Dan Fulani ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da mutanensa
  • Alhaji Abdullahi Dan Fulani ya yi magana kan kafa kungiyar Arewa da za ta goyi bayan Barau da ayyukan alheri da yake yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi bakuncin shugabannin al’ummar Arewa da ke Legas a ofishinsa da ke Majalisar Dokoki ta Kasa a Abuja.

Jagoran tawagar, Alhaji Abdullahi Dan Fulani, ya bayyana wa Sanata Barau ayyukan da al’ummar Arewa ke yi a Legas.

Barau
Sanata Barau ya karbi Hausawan Legas zuwa APC
Asali: Facebook

Sanata Barau Jibrin ya wallafa yadda ziyarar ta gudana a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Wasu mawakan Kannywood sun watse wa Kwankwasiyya, sun kama layin Barau a APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin ganawar, Dan Fulani ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya tare da komawa jam’iyyar APC da mutanensa.

Jagoran 'yan Arewa a Legas ya koma APC

Alhaji Abdullahi Dan Fulani, wanda aka fi sani da “AA Fulani,” ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa APC ne saboda sha’awarsa da irin ayyukan Sanata Barau Jibrin.

Bayan ficewa daga NNPP, Dan Fulani ya sanar da kafa kungiyar Arewa da za ta cigaba da tallafawa wajen yada ayyukkan Sanata Barau da kuma inganta rayuwar 'yan Arewa a Legas.

Sanata Barau Jibrin ya yi maraba da matakin da Dan Fulani da mabiyansa suka dauka, ya na mai jaddada cewa ya na tare da su domin ci gaban al’ummar Arewa.

Sanata Barau ya yi magana kan zaman lafiya

A yayin ganawar, Sanata Barau Jibrin ya yaba da yadda al’ummar Arewa ke zaune lafiya da sauran kabilu a Legas.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a SDP bayan El Rufa'i ya koma cikin jam'iyyar

Ya bukaci su ci gaba da bin doka da oda tare da kare martabar Arewa a duk inda suka tsinci kansu.

Sanatan ya ce zaman lafiya da hadin kai su ne ginshikan ci gaban kowace al’umma, kuma wajibi ne kowa ya zama mai kishin juna.

Ya tabbatar wa da shugabannin al’ummar Arewa a Legas cewa zai ci gaba da goyon bayansu da hadin gwiwa don tabbatar da cigaban yankin da kuma daukaka martabar ‘yan Arewa a Legas.

Barau
Sanata Barau yayin karbar 'yan Kwankwasiyya zuwa APC. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Mabiya Sanata Barau sun nuna farin ciki

Bayan sauya shekar, masoya Sanata Barau Jibrin sun nuna farin cikinsu a karkashin rubutun da ya yi a shafinsa na Facebook.

Wasu daga cikin magoya bayan Sanatan sun bayyana matakin da Dan Fulani da mambobinsa suka dauka a matsayin ci gaba ga jam’iyyar APC.

Ana ganin cewa sauya shekar AA Fulani za ta karfafa jam’iyyar APC a yankin da kuma kara hadin kai a tsakanin al’ummar Arewa da ke Legas.

Kara karanta wannan

Daga sauya sheka, El Rufa'i ya fadi yadda zai jawo rugujewar APC a Najeriya

An samu rikici a jam'iyyar SDP

A wani rahoton, kun ji cewa bayan sauya shekar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi an samu sabani a jam'iyyar SDP.

Shugaban jam'iyyar SDP a jihar Kogi ne ya yi zargin cewa wasu 'yan ba-ni-na-iya na shirin kwace masa ragamar shugabanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng