Buba Galadima Ya Tuna Baya, Ya Bayyana Dalilin Samun Sabani da Buhari
- Buba Galadima wanda a baya yake tare da Muhammadu Buhari ya yi magana kan dalilin da ya sanya suka samu saɓani
- 'Dan siyasar ya ce tsohon shugaban ƙasan ya kafa wani kwamiti domin a kore shi daga APC saboda yana yawan faɗin gaskiya
- Ya ƙara da cewa ganin cewa abin da Buhari yake so ake yi, sai kawai ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Buba Galadima, tsohon makusancin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi magana kan dalilin da ya sanya suka samu saɓani a tsakaninsu.
Buba Galadima ya bayyana cewa sun samu saɓani da Buhari ne saboda bai tsoron faɗin gaskiya.

Asali: Facebook
Jigon na jam'iyyar NNPP ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene abin da ya haɗa Buhari da Buba Galadima?
Buba Galadima ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan ya zarge shi da yawan yin magana da kuma ƙin tsoron faɗin gaskiya.
Ya nuna cewa hakan ne ya sanya Buhari ya kafa wani kwamiti ƙarƙashin Bola Tinubu domin a kore shi daga jam'iyyar APC.
Sannan ya ƙara da cewa da ya ga yadda Buhari yake so haka ake yi, sai kawai ya tattara ƴan kayansa ya bar jam'iyyar kafin a kore shi.
"Ni ba na cikin APC yanzu. Lokacin da Buhari ke mulki, ya kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu, wanda yanzu shi ne shugaban ƙasa, domin a cire sunana daga kwamitin amintattu na APC da kuma daga majalisar ƙoli ta APC."
"An yi hakan ne wai saboda ina yawan magana, kuma ina kallon idonsa ina faɗin gaskiya. Da na ga cewa abin da shugaban ƙasa (Buhari) ke so shi ake yi, sai na bar musu jam’iyyar."
- Buba Galadima
Buba ya faɗi ƙalubalen da ƴan adawa ke fuskanta
Jigon na NNPP ya bayyana cewa ƴan adawa ba su iya taɓuka komai a ƙasar nan saboda babu kuɗaɗe a hannunsu.

Asali: Facebook
"Ta yaya za a ce ‘yan adawa za su yi ƙarfi alhali ba su da kuɗin da za su fuskanci gwamnati? Lokacin da duk kuɗin ƙasar yana hannun masu mulki, ba a hannun jama'a ko ƙasa ba, ta yaya za su ƙarfafa?"
"Na je asibiti a wata ƙasar waje, har na kusa yin kuka. Na je neman magani, don duba wata tiyata da aka yi min a watan Oktoba 2023. Asibitocin Najeriya kamar makabartu ne, idan ka shiga, kamar ka je ne jiran a binne ka."
"Ka ambaci batun ‘yan adawa; da dama suna sauya sheƙa zuwa APC. Ka yi tunanin suna sauya sheƙa ne saboda APC na yin aiki nagari?"
"Ni da kai ba mu da kuɗi, amma su suna da shi kuma bai ishe su ba. Suna so su ci zaɓe su samu ƙarin kuɗi. Kana ganin abin da muke gani? Cewa suna ƙara ƙarfafa masu danniya?"
- Buba Galadima
Buba Galadima ya magantu kan zaɓen 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa ƙuri'u ba su amfani a zaɓen Najeriya.
Buba Galadima ya nuna cewa ba za a samu sahihin zaɓe ba a 2027, idan har.ba gyara aka yi wa dokar zaɓe ba.
Ya yi kira da babbar ga ƴan Najeriya kan su tashi tsaye domin ganin cewa an yi wa dokar zaɓen gyara ta yadda za a samu sahihin zaɓe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng