Maganar Gwamna Zulum Ta Fara Fitowa, Ƴan Ta'adda Sun Ruguza Manyan Gadoji 2
- Rahotanni daga jihar Borno sun nuna cewa ƴan ta'adda sun fara kaddamar da hare-hare kan muhimman kayan gwamnati kamar gadoji
- Ana zargin ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun ruguza gadoji biyu a wani yunƙuri na daƙile ayyukan sojoji da sauran jami'an tsaro
- Wannan al'amari na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan Gwamna Babagana Umaru Zulum ya yi zargin cewa ƴan ta'adda sun farfaɗo da karfinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Ana zargin kungiyoyin ta'addanci watau Boko Haram da ISWAP sun ruguza gadoji biyu da bama-bamai a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kalilan bayan gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya koka kan ƙaruwar hare-haren ƴan ta'adda a jiharsa.

Asali: Facebook
Rahoton jaridar Leadership ya bayyana cewa ƴan ta'adda sun fara farmakar nuhimman kayayyakin gwamnati a jihar Borno kuma sun fara da gadoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram/ISWAP sun ruguza gadoji 2
An ruwaito cewa ƴan ta'addan sun fara maida hankali kan gadoji waɗanda ke da matukar muhimmanci wajen zirga-zirgar jama'a da dakarun hukumomin tsaro a Borno.
Wani dandalin tsaro da leken asiri, Eons Intelligence, ya bayyana a shafinsa na X ranar Laraba cewa hare-haren na nufin hana jami’an tsaro zirga-zirga da kuma kawo cikas ga ayyukan sojoji a yankunan da abin ya shafa.
Ƴan ta'addan sun kai harin farko kan gadar Manda Fuma da ke kusa da Biu, wata hanya mai matukar amfani ga sojoji da fararen hula.
Majiyar ta rubuta cewa:
"’Yan ta’adda sun fara kai hari kan muhimman gine-ginen gwamnati. Gadar Manda Fuma da ke kusa da Biu ce ta fara fuskantar wannan matsala.”
Rusa gadojin zai iya tauye ayyukan sojoji
Baya ga wannan, rahotannin da aka samu duk da ba a tabbatar da su ba, sun nuna cewa an lalata gadar da ke yankin Alaramma a Borno.
An ce maharan sun rushe gadar da ke hada FOB a Wajiroko da Sabon Gari, wanda hakan ke barazana ga zirga-zirgar jami’an tsaro da kai ɗauki da kayan agaji.

Asali: Facebook
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar soji ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da kai hari da lalata gadojin ko akasin hakan ba.
Masana tsaro na ganin wannan sabon salo na kai hare-hare kan gadoji a matsayin yunkuri na kara takura wa dakarun tsaro da hana su gudanar da aiki yadda ya kamata a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.
Ƴan ta'dda sun tashi bam a gada a Borno
A wani labarin, kun ji cewa ƴan ta'adda da ake zargin mayakan ISWAP ns sun tashi bam a kan gadar da ke hanyar Damboa zuwa Biu a jihar Borno.
An ruwaito cewa maharan sun tashi bam din ne da misalin karfe 2:20 na tsaƙar dare ranar 15 ga watan Afrilu, 2025.
Fashewar bam din ta lalata gadar gaba ɗaya, wanda hakan ya katse hanyar da ke haɗa kauyen Mandafuma da garin Biu cikin Jihar Borno.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng