Sabon Salo: Gwamnatin Jigawa Ta Kafa Dokar Sanya Hijabi ga Ma'aikatan Tsaro Mata
- Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sanya Hijabi ga mata ma’aikatan tsaro domin ba su damar bin addininsu da al’adunsu ba tare da katsalandan ba
- Kwamishinan yada labarai a jihar, Sagir Musa, ya ce wannan matakin zai karfafa gwiwar mata 9,969 da aka dauka aiki a kamfanonin tsaro uku masu zaman kansu
- Gwamnati ta kaddamar da makon ƙirƙira da ƙere-ƙere don karfafa matasa a fannonin fasaha, sana’o’i da kirkire-kirkire a fadin jihar Jigawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki muhimmiyar matsaya dangane da tufafin mata ma’aikatan tsaro da ke da damara.
Gwamnatin ta umurci kamfanonin tsaro masu zaman kansu uku da ke aiki a jihar da su ba mata damar sanya hijabi yayin aikin tsaro.

Asali: Facebook
Musabbabin amincewa da dokar hijabi a Jigawa
Wannan sanarwa ta fito ne daga majalisar zartarwa ta jihar ta bakin Kwamishinan yada labarai, Sagir Musa, bayan taron da aka gudanar a Dutse, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin kokarin Gwamna Umar Namadi na samar da yanayi mai dacewa da karbuwa ga kowa, musamman mata.
Sanarwar ta ce:
"Ta hanyar amincewa da sanya hijabi, gwamnati na karfafa wa mata gwiwa wajen bin addini da al’adunsu ba tare da shinge ba."
Kwamishinan ya kara da cewa wannan mataki ya biyo bayan rahoton da kwamitin kula da tsaro a makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar.
Ya ce:
“Wadannan kamfanonin za su bai wa mata damar sanya hijabi a aiki daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki.
"Wannan matakin yana jaddada goyon bayan gwamnati ga manufofin girmamawa da kamun kai da kuma karbuwa a wurin aiki.”

Asali: Original
Musa ya ce wannan umarni zai bai wa matan damar bin addini da al’adu yayin aikin tsaro, kuma zai inganta kwarin gwiwarsu, Daily Post ta ruwaito.
Gwamnan Jigawa ya tallafawa ɗalibai a Cyprus
Bugu da kari, majalisar zartarwa ta amince da fitar da N516.1m don tikitin komawa da tafiya daya ga dalibai 185 na Jihar Jigawa a Cyprus.
Ya ce:
“Wannan taimako yana nuna cikakken goyon bayan gwamnatin Jigawa ga ilimi da jin dadin dalibai da ke kasashen waje, musamman a bangaren lafiya.”
Kwamishinan ya ce matakin gwamnati na tallafa wa daliban lafiya da karfafa kirkire-kirkire na matasa yana nuna himma kan ci gaban dan Adam.
Bugu da kari, majalisar ta amince da kaddamar da makon kirkire-kirkire da kere-kere a jihar Jigawa daga shekarar 2025.
A cewar Kwamishina, wannan shiri na nuna goyon bayan gwamnati ga ci gaban baiwa da nufin bunkasa fasaha da kirkira a tsakanin matasa.
Gwamnan Jigawa ya dauko hanyar inganta noma
Kun ji cewa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da rabon babura 300 ga malaman gona domin saukaka zirga-zirga da wayar da kan manoma.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an raba baburan ne a matsayin rance ba mai kudin ruwa ba, kuma za su biya su ne a cikin watanni 60.
An ce shirin na daga cikin kokarin gwamnati na sauya fasalin harkar noma da tabbatar da wadatar abinci a fadin jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng