Tsohon Gwamna Ya Tafi Wurin Yan Sanda da Natasha Ta Zarge Shi da Karbo Kwangilar Kashe Ta
- Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya shigar da ƙara gaban Sufeto Janar na ‘yan sanda, yana zargin Natasha Akpoti-Uduaghan da bata masa suna
- Natasha ta zargi shi da Gwamna Ahmed Ododo da karɓar umarni daga Sanata Godswill Akpabio domin a kashe ta a mazabar Kogi ta tsakiya
- Lauyoyin Bello sun nemi Natasha ta janye kalamanta tare da bada haƙuri ko kuma ta fuskanci shari'a bisa tuhumar batanci da yada bayanan ƙarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kogi – Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya shigar da kara gaban Sufeto Janar na ‘yan sanda kan zargin batanci da Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa.
A cikin ƙarar da lauyansa, N.A. Abubakar, ya fitar hannu a ranar Laraba, Bello ya nemi rundunar ‘yan sanda ta Najeriya da ta gayyaci Sanata Natasha domin yi mata tambayoyi.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan yana so dakatacciyar Sanatar ta gabatar da hujjojin da suka tabbatar da zargin da ta yi a kansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Natasha ta zargi Yahaya Bello da gwamnan Kogi mai ci, Ahmed Usman Ododo, da karɓar umarni daga shugaban majalisar dattwa, Sanata Godswill Akpabio, domin a kashe ta.
Yahaya Bello ya kai Natasha wurin ‘yan sanda
Jaridar Channels TV ta bayyana cewa tsohon gwamnan ya ce kalaman da Natasha ta furta game da shi ƙarya ne, kuma ta yi su ne domin tada zaune tsaye.
Ya ce kalamanta sun ƙunshi manyan laifuffuka kamar batanci da zargi ba tare da hujja ba da kuma tunzura jama’a, wanda dukkanninsu laifi ne a ƙarƙashin dokokin Najeriya.
A cikin wasikar da aka aika wa ‘yan sanda, lauyan Yahaya Bello ya ce:
“Idan ta gaza gabatar da hujjoji da ke tabbatar da zargin da ta yi, a kama ta, a kuma gurfanar da ita a gaban kotu bisa tanade-tanaden doka kan batanci, tunzura jama’a da yada bayanan ƙarya da ke barazana ga zaman lafiya.”
Yahaya Bello ya tura sako kai tsaye ga Natasha
Tsohon gwamnan ya kuma aika da wata wasika kai tsaye ga Natasha ta hannun lauyoyinsa, Chief R.O. Balogun, SAN & Co, inda ya bukaci ta janye kalamanta.

Asali: Facebook
Haka kuma ya bukaci ta bada haƙuri a bainar jama’a kan kalaman batanci da ta yi masa a cikin jaridun ƙasa guda biyu – ko kuma ta fuskanci matakin shari’a.
A cewar wasikar:
"Sanata Akpoti-Uduaghan ta bata mutuncin abokin mu'amalarmu ta hanyar nuna shi a matsayin ɗan siyasa mai amfani da tashin hankali da daukar fansa, ta kuma ruɗi jama’a da ƙoƙarin tunzura rikicin kabilanci da siyasa musamman tsakanin kabilun Ebira da ma mutanen Kogi ta tsakiya gaba ɗaya.
“Ta tozarta sunansa bisa wani zargi mai nauyi da zai iya cutar da siyasar sa da kuma lafiyar kansa; sannan ta yi amfani da matsayinta a majalisa wajen bazawa jama’a ƙaryar da ba ta da hujja a cikin wani yanayi da ya ɗauki hankali.”
Lauyoyin Bello sun bukaci Sanata Natasha ta daina yin kowane irin furuci da ke ɗauke da batanci ko zargi a kan tsohon gwamnan gaba.
Akpabio ya musanta zargin yunkurin kashe Natasha
A baya, kun samu labarin cewa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar da ƙara gaban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na ƙasa a kan Natasha Akpoti Uduaghan.
Ya shaidawa rundunar, a karkashin jagorancin Kayode Egbetokun cewa zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa na shirin kashe ta, tsagwaron karya da bata suna.
Natasha ta yi zargin ne a ranar 1 ga Afrilu, lokacin da ta kai ziyara garinta da ke jihar Kogi, a nan ne ta shaidawa taron cewa an kammala kitsa yadda za a kashe ta, a dora masu laifin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng