Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

  • Kwanaki bayan gano kisan gillar da aka yiwa Hanifa Abubakar, an samu wani mummunan labari da ya sake faruwa
  • An hallaka wani almajiri a tsangayarsu bayan shafe wani lokaci yana daure ana azabtar dashi a makarantar
  • Gwamnatin jihar Kano ta fusata, ta ce lallai dole ne a dauki matakin domin binciko abin da ya faru a makarantar

Jihar Kano - Daily Trust ta rahoto cewa, gwamnatin jihar Kano ta bukaci a tono gawar wani yaro Almajiri da aka ce malaminsa ya azabtar da shi har ya mutu.

Dakta Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci makarantar da ke unguwar Wailari a jihar Kano, ranar Talata.

Mutum shida da ake zargi da kisan dalibi
Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano | Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari

Ya kara da cewa ‘yan sandan sun kai samame ne a wata haramtacciyar cibiyar gyaran hali a unguwar Naibawa ‘Yan Lemo da ke karamar hukumar Kumbotso.

Sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga SO Kiyawa ta bayyana cewa, an kama wani Musa Safiyanu mai gudanar da cibiyar, inda ake daure yara da kuma azabatar dasu da sunan gyaran hali.

Hakazalika, sanarwar ta ce Abdulladif Musa mai shekaru 18 ya azabtar da wani matashi mai shekaru 22 mai suna Aminu Ado har ya mutu a ranar 29 ga watan Janairu.

A cewar sanarwar:

“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, nan take ya tada tare da umurtar tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Abdulkarim Abdullahi da su sanya ido a kai na sa’o’i 24, su tabbatar da rahoton, su ceto wadanda abin ya shafa da kama masu laifi.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

"Nan da nan tawagar ta fara aiki kuma an gano rahoton gaskiya ne."

Ya kara da cewa a ranar 31 ga watan Junairun shekarar 2022, an gano mutane sama da 113 a tsare kuma a kulle a wani daki.

An samu mutanen da nau'ikan raunuka daban-daban sakamakon azabtarwa wanda tuni aka garzaya da su Asibitin kwararru na Murtala domin yi musu magani kana a mika su ga gwamnatin jihar Kano.

Wadanda ake tuhuma da laifin

  1. Musa Safiyanu, mai shekaru 55 da ke Na'ibawa Yan Lemo a Kano
  2. Abdullatif Musa, mai shekara 18, da ke Na'ibawa Wailari, Kano
  3. Usman Abdulrauf Imam, mai shekaru 19 daga Yanya Abuja
  4. Mustapha Bala, mai shekaru 20 daga Azare, jihar Bauchi
  5. Sadiq Ismail, Unguwa Uku a Kano,
  6. Umar Bako Abdulwahab, mai shekaru 38, a unguwar Kureken Sani, a karamar hukumar Kumbotso jihar Kano

Sanarwar ta ce:

“A binciken farko, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun shafe sama da shekaru goma (10) suna gudanar da cibiyar duk da dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanya."

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Kalli hotunan yadda gidan yake da yadda ake azabtar da yara:

Wannan mummunan labari dai ya biyo bayan kisan da Abdulmalik Tanko, wani shugaban makaranta kudi da ya yi wa dalibarsa Hanifa Abubakar, yarinya mai shekara biyar.

Tanko dai ya sace yarinyar ne kafin ya kashe ta, kamar yadda rahotanni da hirarraki suka tabbatar.

A wani labarin, wata jami'a a jamhuriyar Nijar, Maryam Abacha American University ta sanyawa wani titi sunan Hanifa Abubakar Abdulsalam.

Hanifa Abubakar, wata yarinya mai shekaru 5, an yi mata kisan gilla a jihar Kano, bayan da wani malami kuma shugaban makaranta ya sace ta.

Bayan kisan Hanifa, jama'a da dama sun damu matuka kan labarin, lamarin da ya kai ga tsoma baki daga gwamnatin Kano da ma na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel