An Gano Inda Gwamna Fubara Yake bayan Sojoji Sun Mamaye Fadar Gwamnatin Ribas
- Wata majiya daga fadar gwamnatin Ribas ta tabbatar da Simi Fubara ya na nan cikin gidansa na gidan gwamnati bayan an ayyana dokar ta ɓaci
- A jiya Talata ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Simi Fubara, mataimakiyarsa da dukkan ƴan Majalisar dokokin Ribas
- Jim kaɗan bayan haka, dakarun sojoji da motocin sulƙe suka mamaye fadar gwamnatin da ke Fatakwal, lamarin da ya kara jefa ruɗani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Najeriya a daren Talata, 18 ga watan Maris, 2025.
Bola Tinubu ya sanar da wannan mataki ne yayin wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasa kan halin da jihar Ribas ta tsinci kanta.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Tsohon hadimin Jonathan ya dauko zancen tsige Tinubu kan dakatar da Gwamnan Ribas
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, matakin ya zama dole domin dawo da doka da oda a jihar mai dinbin arzikin man fetur..
Bola Tinubu ya naɗa gwamnatin riko
Sanarwar ta kuma haɗa da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Shugaban ƙasa ya naɗa tsohon hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai jagoranci al’amuran jihar.
Bayan ‘yan sa’o’i kaɗan da sanarwar, sojoji suka mamaye gidan gwamnati da ke birnin Fatakwal.
Ina Gwamna Fubara ya shiga?
Wata majiyar Punch ta bayyana cewa gwamnan na nan a gidansa da ke cikin fadar gwamnati lokacin da sojoji suka mamaye wurin da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
"To, a halin da ake ciki yanzu, akwai sojoji a cikin gidan gwamnati amma gwamna ya na nan a gidansa da ke fadar gwamnati, ya yi zamansa."

Asali: UGC
Har ila yau, an girke wata motar sulƙe ta yaƙi (APC) a ƙofar shiga fadar gwamnati, tana kallon babban titin da ke gabanta.
Wani ɗan jarida da ya ziyarci wurin da misalin ƙarfe 9:00 na dare ya ga motocin alfarma (SUVs) da dama a gaban ƙofar gidan gwamnati, masu fitilu a kunne.
Sai dai babu tabbacin ko gwamnan yana shirin barin gidan gwamnati ne ko akasin haka.
Halin da ake ciki bayan dakatar da Fubara
A cikin birnin Fatakwal, an ga jama’a da direbobi na hanzarta komawa gidajensu bayan sun ji sanarwar ayyana dokar ta-baci.
Haka nan, mutane da yawa sun taru a kan tituna suna tattauna batun, inda wasu suka nuna damuwa da takaici game da lamarin, suna zargin ‘yan siyasa da haddasa rikicin da ya kai ga wannan mataki.
Ribas: PDP ta yi watsi da matakin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi fatali da matakin ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Babbar jam'iyyara dawa ta ƙasa ta bayyana cewa dakatar da Fubara da naɗa wanda zai jagoranci gwamnatin riko a Ribas ya saɓawa kundin tsarin mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng