An yi Rubdugu wa Sanata Shehu Sani kan Goyon Bayan Dakatar da Fubara
- Bayan dakatar da gwamna Simi Fubara, Sanata Shehu Sani ya ce dokar ta-baci ita ce kadai mafita don dawo da doka da oda a Rivers
- Biyo bayan lamarin, wasu matasa sun caccaki Shehu Sani, suna zargin cewa an yi amfani da dokar ne don cimma muradin siyasa
- Wasu daga cikin matasan da suka yi raddi, sun ce rashin dakatar da Nyesom Wike yana nuna cewa ba adalci a matakin da aka dauka
- Wani matashi ya bayyanawa Legit cewa abin da ya faru da Shehu Sani izina ne ga sauran 'yan siyasa masu tasowa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa dokar ta-baci ita ce kadai mafita don dawo da zaman lafiya a jihar.
Sai dai matasa sun yi kaca-kaca da Sanata Shehu Sani, su na kalubalantar ra'ayin da ya bayyana a matsayinsa na dan gwagwarmaya.

Asali: Facebook
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shehu Sani ya ce an yi kokarin warware rikicin ta hanyar shari’a, siyasa, har ma da hanyoyin addini, amma hakan ya ci tura.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya kare matakin Bola Tinubu
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa matakin shugaba Tinubu na kafa dokar ta-baci a Jihar Rivers shi ne kadai hanyar tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce rashin samar da mafita ta hanyoyin shari’a da siyasa ya sanya dole a dauki matakin gaggawa domin kare martabar jihar.
A cewarsa, Rivers tana da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya, don haka ba za a bar rikicin ya ci gaba ba.

Asali: Facebook
Matasan sun yi rubdugu wa Shehu Sani
Wani matashi, Abdulaziz A. Galadima, ya soki matakin, yana mai cewa gwamnatin tarayya ba ta taba neman sahihin mafita ba.
Matashin ya yi zargin cewa:
"Ana amfani da dokar ne kawai don tabbatar da mulkin mallaka a Jihar Rivers, ba don dawo da doka da oda ba."
Shi ma Yusuf Isa ya ce:
"Idan rikicin ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya ba su sa gwamnati ta kafa dokar ta-baci ba, amma hare-haren bututun mai suka haddasa hakan,
"To a fili take cewa mulkin Tinubu yana fifita bututun mai da muradin Wike fiye da jin dadin jama’a."
Umar Saeed Yushau ya mayar da martani ga Sanata Shehu Sani da cewa:
"Je ka nemi wadanda za ka yaudara, ba mu ba."
Shi ma Adam Nasir Uthman ya yi martani wa Shehu Sani da cewa:
"Da a ce ka na a dayan bangaren siyasar, ('Cikin 'yan adawa) da wata maganar daban za ka yi."
Bashir Lamido ya bayyana cewa dakatar da Gwamna Fubara da sauran jami’an gwamnati da barin Nyesom Wike yana nuna cewa akwai son rai a matakin.
Mohammed Sulaiman Sani ya ce:
"Neman na abinci!"
Legit ta tattauna da Aminu Isa
Wani matashi dan jam'iyyar PDP, Aminu Isa ya ce ya goyi bayan abin da matasan suka yi wa Sanata Shehu Sani.
"Haka ya kamata a rika yi wa 'yan siyasa da ba su da akida, ya kamata duk wanda zai tsaya a kan gaskiya to ya tsaya a kanta ko da yaushe."
- Aminu Isa
Gwamna Fubara ya yi bayanin farko
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi jawabi na farko bayan Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi.
Gwamna Fubara ya bukaci al'ummar jihar da su cigaba da bin doka da oda tare da tabbatar musu da cewa zai dauki dukkan matakin da ya dace kan lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng