Jami’an ’Yan Sanda A Katsina Sun Yi Karin Haske Kan Matar Da Aka Kama Da Harsasai

Jami’an ’Yan Sanda A Katsina Sun Yi Karin Haske Kan Matar Da Aka Kama Da Harsasai

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina sun yi karin haske kan cafke wata mata da aka yi da harsasai masu tarin yawa a jihar
  • An kama matar ce wacce mijinta soja ne bayan samun ta da harsasai a cikin jaka yayin da ta bar Bauchi zuwa Katsina
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce matar ta samu sabani da mijinta inda cikin fushi ta dauki jakar mijinta ba tare da sanin akwai harsasai ba

Jihar Katsina – Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kama wata mata dauke da harsasai masu tarin yawa a cikin jaka.

Matar wanda ba a bayyana sunan ta ba an tabbatar da cewa matar wani soja ne da ke jihar Bauchi.

'Yan sanda sun kama wata mata da harsasai a jihar Katsina
'Yan Sanda a Katsina Sun Yi Martani Kan Matar da Aka Kama da Harsasai. Hoto: @ZagazOlaMakama.
Asali: Twitter

Me ye aka kama matar da shi a Katsina?

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

Zagazola Makama ya bayyana haka ne a shafin Twitter inda ya ce matar an cafke ta ne a jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya tabbatar da matar ta samu matsala da mijin nata wanda jami’in soja ne inda ta dauki jakarsa cikin fushi don barin gidansa.

Ta zuba kayan sakawa a cikin jakarsa ba tare da sanin cewa akwai harsasai masu yawa a cikin ba, KOKO TV ta tattaro.

Meye 'yan sanda su ka ce kan matar a Katsina?

Rundunar ta ce matar ta baro Bauchi don zuwa Katsina saboda sabanin da su ka samu da mijinta kafin aka kamata a tashar mota.

Bayan kwakkwaran bincike, matar ta bayar da lambar daya daga cikin ‘yan uwanta da ke Katsina inda aka gayyace su ofishin don amsa tambayoyi.

Daga bisani ‘yan uwan matan sun sanar da mijin wanda soja ne halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Tattakin Neman Yanci": Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Zuwa

Mijin ya kai rahoto inda aka dauke maganar daga hannun ‘yan sanda zuwa ga rundunar sojoji da ke jihar Katsina.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama mijin kuma har yanzu ya na hannun ‘yan sanda saboda zargin sakaci da kuma wasa da aiki.

An cafke dalibai 6 kan zargin kashe abokinsu a Katsina

A wani labarin, jami'an tsaro sun cafke wasu dalibai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsen-Ma kan zargin hallaka abokinsu kan budurwa.

Marigayin mai suna Abubakar Nasir Wanda bai wuce shekaru 21 ba ya rasa ransa kan wata budurwa 'yar makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel