Halin da Janar Tsiga ke ciki a hannun Ƴan Bindiga duk da Karbar Miliyoyi na Fansa
- Ƴan bindiga na ci gaba da riƙe Janar Maharazu Tsiga a garin Tsiga da suka sace a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina tun kwanakin baya
- Duk da biyan kudin fansa mai yawa, masu garkuwa da Janar Tsiga sun ki sakinsa, kuma sun sake neman karin kudi a wurin Iyalansa
- Tun farko, sun bukaci N250m, daga bisani sun ci gaba da ƙara kudin a yayin tattaunawa da iyalansa har aka biya miliyoyi da ba a bayyana ba
- Kungiyoyin dattawan ACF da KEF sun roki gwamnati da sojoji su ƙara ƙaimi wajen ceto Janar Tsiga da sauran bayin Allah da ke hannun miyagu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bakori, Katsina - Janar Maharazu Tsiga mai ritaya ya na ci gaba da kasancewa a hannun yan bindiga bayan biyan kudin fansa.
An sace Janar Tsiga tare da wasu mutane tara a Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina a ranar 5 ga Fabrairun 2025.

Asali: Facebook
Wane hali Janar Tsiga ke ciki a hannun yan bindiga?
Daily Trust ta gano cewa, masu garkuwa da shi har yanzu na riƙe da shi duk da karɓar kuɗin fansa mai yawa daga hannun iyalansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsiga tsohon Darakta-Janar ne na Hukumar NYSC ta ƙasa kafin ya yi ritaya daga aikin soja.
Wani na kusa da danginsa ya ce yan bindigar sun yi shiru na mako guda bayan biyan kudin, sai daga baya suka ba Janar damar magana da iyalansa.
Ya ce:
“Saboda wasu dalilai, ba zan bayyana adadin kudin da muka biya ba, amma ku tabbata kudin da yawa ne.
“Bayan mako guda suka kira, suka bar shi ya yi magana da mu, amma har yanzu ba su sako shi ba, kuma sun buƙaci ƙarin kudi.”

Asali: Twitter
Janar Tsiga: Miliyoyi da masu garkuwa suka nema
A farko, masu garkuwa sun nemi N250m a matsayin kudin fansa, daga nan kuma aka ci gaba da tattaunawa da ƙarin buƙatu.
An yi imani cewa an mayar da Janar Tsiga wani sabon wuri, don haka matsin lamba ya ƙaru a kan jami’an tsaro da su ƙara ƙoƙari.
Kungiyar ACF da ta dattawan Katsina (KEF) sun nemi gwamnatin tarayya da sojoji su hanzarta ceto Janar ba tare da wata illa ba.
Hakan ya jawo fargaba da zaman dar-dar musamman a yankunan da yan bindiga suke addabarsu bayan sace Janar Tsiga duba da cewa shi tsohon soja ne a Najeriya.
Al'umma na cikin firgici bayan sace Tsiga
Kun ji cewa al'umma yankin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina, na ci gaba da alhini kan sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga da aka sace fiye da wata guda.
An sace tsohon Darakta-Janar na hukumar NYSC tun a farkon watan Faburairun shekarar 2025 da muke ciki wanda ta tayar da kura musamman a Arewacin Najeriya.
Majiyoyi sun bayyana cewa mutane da dama sun yi ƙaura daga gida saboda tsoron da ya shiga zukatansu sakamakon ayyukan 'yan bindiga da suka addabe su a yankunan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng