Wata Mata Ta Rasu a Wani irin Yanayi yayin Tafsirin Kur'ani a Abuja

Wata Mata Ta Rasu a Wani irin Yanayi yayin Tafsirin Kur'ani a Abuja

  • Wata matar aure mai shekara 42 da ake kira Maman Zainab ta fadi, ta mutu yayin tafsirin azumin Ramadan a masallaci a Abuja
  • Wani mazaunin Gawu ya ce matar ta je masallaci cikin koshin lafiya tare da makwabta uku kafin ta fara jin jiri da ciwon kai
  • Da ta fadi, wasu mata suka garzaya da ita asibiti a Gawu Babangida, a nan aka tabbatar da rasuwarta kafin a kai ga ba da taimako
  • Likitan asibitin ya bayyana cewa hawan jini ne ya jawo mutuwar matar, kuma an birne ta bisa sharuddan addinin Musulunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Jama'a sun shiga jimami bayan mutuwar wata matar aure yayin da ake tafsiri a birnin Abuja.

Matar mai shekara 42 da aka bayyana da Maman Zainab, ta fadi yayin tafsirin Ramadan a masallaci a Gawu, Abaji da ke birnin.

Kara karanta wannan

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya daga Indiya duk da tsananin rashin lafiya

Abin tausayi ya faru a masallaci bayan mutuwar mata ana tafsiri
Mata ta rasu ana tsaka da tafsirin Alkur'ani a Abuja. Hoto: Emmanuel Osodi/Majority World/Universal Images Group via Getty Images).
Asali: Getty Images

Yadda mutumi ya rasu ana tsaka da sallah

Wani mazaunin Gawu, Ismail Bala, ya shaida wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:23 na safe a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan ruwaito muku cewa Allah ya karbi rayuwar wani mutum ɗan kimanin shekara 52 mai suna Salihu Byezhe.

Bawan Allah ya rasu ne bayan ya faɗi ana tsakiyar sallar Asuba a Abuja kamar yadda wani mazaunin Gudaba, Musa Dantani ya tabbatar.

Ya ce Salihu ya ɗauki azumi kamar yadda aka saba bayan kammala sahur kafin rasuwarsa inda ya ce tuni dai aka yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

An yi rashi bayan rasuwar mata ana tafsirin Alkur'ani a Abuja
Wata mata ta ce ga garinku yayin da ake tafsirin Alkur'ani a Abuja. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mata ta rasu ana tsaka da tafsirin Alkur'ani

Ismail ya ce matar ta fita daga gida lafiya tare da wasu makwabta uku domin halartar tafsir da ake yi a lokacin azumin Ramadan.

Ya ce matar ta rada wa daya daga cikin makwabtanta cewa tana jin jiri da ciwon kai mai tsanani kafin ta tashi domin fita.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Allah ya karbi rayuwar malamin Musulunci, Idris Dutsen Tanshi

Bayan ta tashi, kafin ta kai kofa ta fadi a cikin masallacin, inda wasu mata suka ruga da ita asibiti domin samun taimako.

Shaidun gani da ido sun ce an garzaya da ita asibitin Gawu Babangida, amma kafin a kai, likita ya tabbatar da mutuwarta, cewar Sahara Reporters.

Shaidun sun kara da cewa:

"Ta je tafsir tare da makwabta a masallacin da ke gaban gidansu kafin ta fadi a ciki, abin takaici, tana isowa asibiti ne rai ya yi halinsa."

Likitan da ya duba lafiyarta ya danganta mutuwarta da hauhawar jini bayan ya gudanar da wasu bincike a jikinta.

Ismail ya ce an birne gawarta a ranar da ta mutu bisa ka’idojin Musulunci, kamar yadda ya dace da addinin.

Yar TikTok daga Najeriya ta mutu a gidanta

Mun ba ku labarin cewa Kamfanin Teleperformance a Kenya ya musanta zargin hana wata ƴar TikTok, Ladi Olubunmi, izinin zuwa hutunta a gida Najeriya.

Kara karanta wannan

'Mun sha azaba': Janar Tsiga ya magantu, ya fadi dabbobin da suke kwana tare da su

An tsinci gawar Olubunmi a cikin gidanta bayan kwana uku da rasuwarta, inda ta riga mu gidan gaskiya a wani yanayi mai ban tausayi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng